Ondo: Jam'iyyar APC Za Ta Bayar da Satifiket Din Lashe Zaben Fidda Gwani

Ondo: Jam'iyyar APC Za Ta Bayar da Satifiket Din Lashe Zaben Fidda Gwani

  • Jam'iyyar APC mai mulki za ta gabatar da satifiket ɗin lashe zaɓen fidda gwanin gwamnan jihar Ondo, ga Gwamna Lucky Aiyedatiwa
  • Mataimakin sakataren tsare-tsaren jam'iyyar na ƙasa ne ya tabbatar da cewa za a ba gwamnan satifiket ɗin ne a ranar Litinin, 29 ga watan Afirilun 2024
  • Gwamnan shi ne dai ya zama ɗan takarar gwamnan jam'iyyar a zaɓen da za a gudanar a watan Nuwamban 2024

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Ondo - Jam’iyyar APC za ta miƙawa wanda ya lashe zaɓen fidda gwani na gwamnan jihar Ondo, Gwamna Lucky Aiyedatiwa, satifiket ɗin lashe zaɓe a ranar Litinin.

Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya yi nasarar lashe zaɓen ne wanda aka gudanar domin fidda ɗan takarar jam'iyyar APC a zaɓen gwamnan jihar na watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

Edo: Babban jigon APC ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar PDP ana shirin zaɓen gwamna

APC za ta gwamnan Ondo satifiket
Gwamna Lucky Aiyedatiwa zai karbi satifiket din lashe zaben fidda gwanin gwamnan Ondo Hoto: Hon. Lucky Orimisan Aiyedatiwa
Asali: Facebook

Mataimakin sakataren tsare-tsaren jam’iyyar na ƙasa, Nze Duru ne ya bayyana hakan ga jaridar The Punch a ranar Lahadi, 28 ga watan Afirilun 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yaushe APC za ta bada satifiket?

"Eh ranar Litinin ne za a gabatar da takardar shaidar cin zaɓen ga Gwamna Lucky Aiyedatiwa a sakatariyar jam'iyyar ta ƙasa da ke Abuja."

- Nze Duru

Sai dai Duru bai bayyana ko za a gabatar da satifiket ɗin ne a gabanin taron kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC) ko a lokacin taron ko bayan an kammala, wanda shi ma za a yi a ranar Litinin.

Hakan dai na zuwa ne kwanaki uku bayan da shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi kira ga ƴan takarar da suka fafata a zaɓen da su marawa Gwamna Lucky Aiyedatiwa baya.

Ondo: Lucky ya yi sa'ar tikitin APC

Kara karanta wannan

Zaben Ondo: Jigon APC ya hango rashin nasara ga jam'iyya, ya bayyana dalili

Kwamitin zaɓen fidda gwanin ƙarƙashin jagorancin Gwamna Usman Ododo ne ya ayyana Ayiedatiwa a matsayin wanda ya lashe zaɓen, bayan kammala gudanar da zaɓen a dukkanin ƙananan hukumomin jihar 18.

Sai dai, wasu daga cikin ƴan takarar sun ƙalubalanci sakamakon zaɓen bisa zargin tafka maguɗi da tashe-tashen hankula a wasu rumfunan zaɓe.

APC za tayi rashin nasara a Ondo?

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani jigo a jam'iyyar APC a jihar Ondo, ya hango rashin nasara ga jam'iyyar a zaɓen gwamnan jihar.

Bamidele Oloyeloogun ya yi nuni da da cewa APC ka iya yin rashin nasarar ne idan ba a soke zaɓen fidda gwani na gwamna da ta yi ba a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel