An Sanya Ranar Fara Binciken Abdullahi Umar Ganduje a Jihar Kano

An Sanya Ranar Fara Binciken Abdullahi Umar Ganduje a Jihar Kano

  • Kwamitin da zai binciki gwamnatin tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, zai fara zamansa a ranar Litinin, 29 ga watan Afirilu
  • Kwamitin binciken shari'ar zai binciko yadda aka karkatar da kadarorin gwamnati a gwamnatin da ta gabata a jihar
  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya ƙaddamar da kwamitocin guda biyu domin binciko abubuwan da suka faru a gwamnatin Ganduje

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Kwamitin binciken shari'a kan zarge-zargen da ake yi wa Abdullahi Umar Ganduje, zai fara zamansa a ranar Litinin, 29 ga watan Afirilun 2024.

Gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf ne ya kafa kwamitin domin binciken yadda aka karkatar da kadarorin gwamnati a lokacin gwamnatin da ta gabata ta Ganduje.

Kara karanta wannan

Neja: Tsohon sakataren gwamnati ya riga mu gidan gaskiya, Gwamna ya tura sako

Za a fara binciken Ganduje
Ranar Litinin za a fara binciken Ganduje a Kano Hoto: @OfficialAPCNg, @Kyusufabba
Asali: Twitter

A ina kwamitin Ganduje zai zauna?

Sakataren kwamitin, Salisu Mustapha, shi ne ya bayyana hakan a cikin wata wasiƙa da ya aika ga darakta janar na yaɗa labarai da wayar da kan jami'a na gidan gwamnatin Kano, a ranar Asabar, cewar rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zaman kwamitin zai gudana ne a babbar kotu ta uku a cikin sakatariyar Audu Bako da misalin ƙarfe 10:00 na safe, rahoton jaridar Nigerian Tribune ya tabbatar.

An ƙaɗdamar da kwamitin binciken Ganduje

A farkon wannan watan ne Gwamna Abba ya ƙaddamar da kwamitocin binciken shari'a guda biyu (JCIs) domin binciken karkatar da kadarorin gwamnati tsakanin shekarar 2015 zuwa 2023.

Kwamitocin za su kuma binciki tashe-tashen hankula na siyasa da mutanen da suka ɓace daga shekarar 2015 zuwa 2023.

A wajen ƙaddamar da mambobin kwamitocin, Gwamna Abba ya sha alwashin hukunta duk wanda aka samu da hannu a ciki.

Kara karanta wannan

Uba Sani v El-Rufai da jerin Gwamnatoci masu mulki da ke binciken gwamnonin Baya

Alƙalan manyan kotunan jihar, mai shari'a Farouq Adamu da Zuwaira Yusuf, su ne za su jagoranci kwamitocin guda biyu.

Kwamitocin sun kuma ƙunshi wasu manyan mutane a jihar a matsayin mambobi domin gudanar da binciken.

Batun neman tsige Ganduje a APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar 'Concerned North Central APC Stakeholders' ta nesanta kanta daga zanga-zangar neman shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi murabus.

Ƙungiyar ta ce wasu korarrun mambobinta ne da aka ba su kuɗi suka shirya gudanar da zanga-zangar ta neman murabus ɗin Ganduje.

Asali: Legit.ng

Online view pixel