Yahaya Bello: Samuel Ortom Ya Shawarci Tsohon Gwamnan Kogi Kan Binciken EFCC

Yahaya Bello: Samuel Ortom Ya Shawarci Tsohon Gwamnan Kogi Kan Binciken EFCC

  • Tsohon gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom, ya shawarci Yahaya Bello da ya fito daga ɓoyon da ya yi ya kai kansa ga hukumar EFCC
  • Samuel Ortom ya bayyana cewa wasan ɓuyan da tsohon gwamnan na jihar Kogi yake yi zai jawo abin kunya ga tsofaffin gwamnoni a ƙasar nan
  • Yahaya Bello dai ya ƙi amsa gayyatar da hukumar yaƙi da cin hanci da rasahwan ta yi masa kan zargin karkatar da maƙudan kuɗaɗe

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Benuwai - Tsohon gwamnan jihar Benuwai, Samuel Ortom, a ranar Lahadi, ya buƙaci takwaransa na jihar Kogi, Yahaya Bello, da ya fito daga maɓoyarsa, ya amsa gayyatar hukumar EFCC.

Yahaya Bello dai ya daɗe yana taƙun saka tsakaninsa da hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC, kan zargin karkatar da N80.2bn.

Kara karanta wannan

Yahaya Bello: Lauya ya hango kuskuren hukumar EFCC, ya yi gargadi

Samuel Ortom ya shawarci Yahaya Bello
Samuel Ortom ya bukaci Yahaya Bello ya mika kansa ga EFCC Hoto: Alhaji Yahaya Bello, Fr. Hyacinth Iormen Alia
Asali: Facebook

Wasan tseren EFCC da Yahaya Bello

Hukumar ta ayyana tsohon gwamnan a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo bayan ya ƙi bayyana a gaban kotu kan ƙarar da ta shigar a kansa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar Punch ta ce da yake jawabi a cocin Redeemed Christian Church of God da ke Makurdi a jihar Benuwai a yayin bikin godiya da muƙarrabansa suka shirya na cikarsa shekara 63, Ortom ya shawarci Yahaya Bello da ya fito daga ɓoyon da ya yi.

Wace shawara aka ba Yahaya Bello?

Ya ce ci gaba da wasan ɓuyar da Yahaya Bello yake yi zai jawowa tsofaffin gwamnonin abin kunya a ƙasar nan, rahoton da jaridar Vanguard ya tabbatar.

"Ina so in yi amfani da wannan damar in shawarci ƙanina kuma abokina, Gwamna Yahaya Bello, da kada ya tozarta tsofaffin gwamnoni."

Kara karanta wannan

Malam El-Rufai zai kara da Tinubu a zaben shugaban ƙasa a 2027? Gaskiya ta bayyana

"Ba ka buƙatar ɓoyewa. Ba ka buƙatar ƙin yadda a kama ka ko wani abu. Ka je ka amsa gayyata. Jami'an EFCC mutane ne. Idan suna yin tambayoyi, akwai dokoki."
"Na yi ƙoƙarin kiransa a waya, amma ban same shi ba. Na gwada na kusa da shi amma ban samu ba. Domin haka ina so a lura da wannan. Duk inda yake idan ya ji ni, Allah ya sa akwai ƴan jarida suna nan, ya kamata ya fito."

- Samuel Ortom

Yahaya Bello ya ƙalubalanci EFCC

A wani labarin kuma, kun ji cewa ofishin yaɗa labarai na Yahaya Bello ya yi iƙirarin cewa hukumar EFCC ba ta taɓa gayyatar tsohon gwamnan na jihar Kogi ba.

Ofishin ya ƙalubalanci hukumar yaƙi cin hanci da rashawan da ta nuna shaidar cewa ta taɓa gayyatar tsohon gwamnan domin yi masa tambayoyi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel