Latest
An tafka babban rashi yayin da matashiyar mawakiya wacce ta kware a wakokin yabo, Morenikeji Adeleke ta riga mu gidan gaskiya a jiya Asabar 27 ga watan Afrilu.
Miyagun 'yan bindiga sun hari a wasu kauyukan jihar Neja inda suka kwashe kayan abinci da sauran kayayyaki masu amfani. Mutanen kauyukan sun tsere.
Tsohon ministan harkokin waje, Ambasada Aminu Bashir Wali ya bayyana yadda tsohon shugaban kasa a mukin soja, Janar Murtala Mohammed ya mutu bai bar komai ba.
Jam'iyyar PDP ta lashe dukkan kujerun ciyamomi 33 a zaben kananan hukumomin jihar Oyo da aka gudanar a ranar Asabar, 27 ga watan Afrilu, sai dai APC ta yi martani.
Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya ce ziyarar da gwamnonin Arewa suka kai Amurka ta fallasa jahilcinsu ga kundin tsarin mulkin Najeriya.
Lauya kuma dan gwagwarmaya, Deji Adeyanju, ya yi gargadin cewa idan hukumar EFCC ba ta yi taka tsan-tsan ba, za ta iya rusa shari'ar Yahaya Bello.
Shugaba Bola Tinubu ya amince ana wahala a Najeriya, amma ya ce daina biyan tallafin fetur shi ne kawai matakin da zai kare Najeriya daga fadawa cikin fatara.
Tsohon shugaban jam'iyyar APC, Sanata Adams Oshiomole ya caccaki tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello da yaronsa, Gwamna Usman Ododo kan saɓa dokar ƙasa.
Gwamna Siminalayi Fubara, na jihar Ribas ya yi alwashin cewa ba zai mulki jihar ba ta hanyar durkusawa wani ba. Gwamnan na rikici da Nyesom Wike.
Masu zafi
Samu kari