Wahalar Man Fetur Ta Jawo Tashin Farashin Motoci da Sauran Abubuwan Hawa

Wahalar Man Fetur Ta Jawo Tashin Farashin Motoci da Sauran Abubuwan Hawa

  • Mazauna Ilorin babban birnin jihar Kwara sun koka kan yadda tsadar farashin ababen hawa ya karu sakamakon wahalar man fetur
  • Mutane da dama sun bayyana yadda suka shiga damuwa ciki har da dawowa tafiya da kafa sakamakon ninkiwa da kudin ya yi
  • An ruwaito cewa gidajen mai da yawa a garin basu bude ba sai dai 'yan bumburutu ne kawai suke cin karensu ba babbaka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kwara - Rahotanni da ke fitowa daga jihar Kwara sun nuna cewa farashin ababen hawa ya karu sakamakon wahalar man fetur.

Fuel station
Tsadar mai ta kara jefa mutane cikin kunci a jihar Kwara. Hoto: Getty Image
Asali: Getty Images

Wahalar fetur yana wahalar da jama'a

Mazauna Ilorin, babban birnin jihar sun bayyanawa manema labarai yadda lamarin ke kokarin durkusa musu lamuran yau da kullum.

Kara karanta wannan

Yadda rashin ruwa yake barazana ga rayuwa da masu sana'o'i a jihar Sokoto

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wani rahoton da jaridar the Guardian Nigeria ta fitar ya bayyana cewa farashin kudin ababen hawa ya ninka a birnin Ilorin tun biyo bayan cire tallafin man fetur.

Amma a halin yanzu kudin ya karu sakamakon wahalar mai da ta kunno cikin kasar daga satin da ya gabata.

Jiya da yau: Farashin abin hawa a Ilorin

An ruwaito cewa daga Olunlade zuwa Offa Garage, wanda a baya ake biyan N100 yanzu sai an biya N200.

Daga Offa Garage zuwa kasuwar Mandate, da ake biyan N200 yanzu ya dawo N400, cewar jaridar Premium Times

Halin da mutane suka shiga kan fetur

Wata mata mai suna Grace Philip ta bayyana cewa kudin abin hawa ya jawo dalilin takaita mata sayayyar da ta je kasuwa.

Ta koka kan yadda farashin ya ninka sakamakon rashin man fetur duk da cewa ana rade-radin saukar farashin mai din kwanakin baya.

Kara karanta wannan

"Abin da ya zama dole ne": Gaskiyar dalilin da ya sa Tinubu ya janye tallafin man fetur

Wata mata mai suna Aisha Muhammad ta ce tashin farashin ababen hawan ya tilasta mata tafiya da kafa zuwa inda za ta je.

Wani mazaunin garin mai suna Umar Haroon ya ce tashin farashin ababe hawa zai kawo cikas ga lamura sosai musamman ga dalibai.

Ya ce lalle dalibai za su gaji sosai idan suka yi tafiya da kafa zuwa makaranta ta yadda ba lalle su fahimci karatu sosai ba.

Farashin man fetur a Ilorin

Rahotanni sun tabbatar da cewa babu gidajen mai da suka bude sosai a cikin garin wanda hakan ne ya kara ta'azzara matsalar.

Kuma farashin mai ya kai daga N750 zuwa N900 a gidajen mai yayin da 'yan bumburutu suke saidawa N1000 zuwa N1,500 duk lita.

Fetur: Gwamnatin Jigawa ta dauki mataki

A wani rahoton kun ji cewa gwmantin jihar Jigawa ta kafa dokar ko-ta-kwana a gidajen mai a fadin jihar sakamakon wahalar mai da ake fama da ita.

Rahotanni sun tabbatar da cewa kwamitin ya fara aiki amma sai dai a hirar da Legit ta yi da mazauna garin sun ce har yanzu basu gani a kasa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel