Yadda Rashin Ruwa Yake Barazana Ga Rayuwa da Masu Sana’o’i a Jihar Sokoto

Yadda Rashin Ruwa Yake Barazana Ga Rayuwa da Masu Sana’o’i a Jihar Sokoto

  • Tsanannin rashin ruwa ya jefa sana'o'i da dama cikin damuwa a jihar Sokoto har wasu kamfanoni na kokarin kullewa
  • Kungiyar masu hada bulo, kamfanin hada ruwan leda da gidajen wanka suna cikin wadanda matsalar ke yiwa barazana
  • Wadanda abin ya shafa sun bayyana irin halin da suka samu kansu a ciki da kuma matakan da za su dauka domin samun mafita

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Sokoto - Masu kamfanoni da sana'o'in da ke da alaka da ruwa sun koka kan yadda rashin ruwa ke barazana ga ayyukansu a jihar Sokoto.

Sokoto governor
Karancin ruwa ya sa gwamnatin Sokoto ta yankewa kamfanoni ruwa. Hoto: Ahmed Aliyu Sokoto
Asali: Facebook

Barazanar na zuwa ne a lokacin da masu sana'ar samar da ruwan leda, wankin mota, gidajen wanka da bahaya da buga bulo suka bayyana cewa gwamnati ya yanke musu ruwa.

Kara karanta wannan

Wahalar man fetur ta jawo tashin farashin motoci da sauran abubuwan hawa

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa hukumar samar da ruwan sha a jihar ce ta yanke ruwa ga kamfanonin a wurare da dama cikin fadin jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan kamfanonin rahotanni sun tabbatar da cewa hukumar ta yanke ruwa ga gidajen da suke da manyan abubuwan adana ruwa.

Yanke ruwa: Jawabi daga gwamnati

A lokacin da shugaban hukumar samar da ruwa a jihar, Alhaji Sama'ila Umar Sa'id, yake bayani a kan dalilin yanke ruwan, ya ce sun yi haka ne domin samar da ruwa a gidaje domin amfanin yau da kullum kafin kamfanoni.

Bincike ya nuna cewa daukar matakin yana da alaka da tsananin rashin ruwa da al'ummar Arewa suka shiga ciki a kwanannan.

Halin da masu buga bulo suka shiga

Shugaban kungiyar masu buga bulo a jihar, Alhaji Kabiru Rumbukawa, ya ce matakin da hukumar ta dauka ya durkusar da ayyukan su.

Kara karanta wannan

"Shi ke haukata 'yan kasa", Malamin addini a Kaduna ya ja kunnen Tinubu kan halin kunci

A cewarsa, mafi yawan kamfanonin buga bulo a jihar sun dogara ne da ruwan famfo kuma a halin yanzu ba za su iya sayan ruwa daga bohol ba, cewar Peoples Gazette Nigeria

Kamfanin ruwa ya koka kan rashin ruwa

Shugaban kungiyar kamfanin ruwan leda na jihar, Alhaji Nasiru Garka, ya bayyana takaici a kan matakin da gwamnatin ta dauka.

Ya kara da cewa ba a basu wata sanarwa kafin yanke musu ruwan ba kuma za su tinkari hukumar domin jin dalili.

Masu wankin mota sun koka kan ruwa

Masu sana'ar wankin mota a fadin jihar sun ce abin ya kawo musu tsaiko cikin harkokinsu wurin takaita musu ayyukan da suke yi a kullum.

Wani mai wankin mota, Malam Dahiru Garba ya ce lalle suna biyan kudin ruwa akai-akai amma basu san dalilin yanke musu ruwan ba.

Matsalar ruwa ta yi ƙamari a Arewa

A wani rahoton kun ji cewa matsalar ruwan sha ta yi ƙamari a garuruwan Arewa da dama ciki har da Gombe, Kano, Yobe da Adamawa.

Rashin ruwan ya shafi ayyukan al'umma da harkokin ibada ta inda mutane ke neman rufe wuraren ayyuka saboda rashin ruwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel