Shugaban Hukumar JAMB, Zai Yi taro a Kan Sakamakon Jarrabawar UTME 2024

Shugaban Hukumar JAMB, Zai Yi taro a Kan Sakamakon Jarrabawar UTME 2024

  • Hukumar shirya jarrabawar shiga makarantun gaba da sakandare ta JAMB ta kammala shirin sakin sakamakon jarrabawar UTME
  • Kimanin dalibai miliyan 1.9 ne su ka zauna jarrabawar da aka shafe kusan mako guda ana yi a cibiyoyin UTME da ke sassan kasar nan
  • Farfesa Ishaq Oloyede a Litinin din nan zai gana da manema labarai a birnin tarayya Abuja, inda ake sa ran sakin sakamakon jarrabawar a yau

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja - Hukumar shirya jarrabawar shiga makarantun gaba da Sakandare (JAMB) ta yi tsokaci kan ranar da za ta saki sakamakon jarrabawar UTME da dalibai kimanin 1.9 miliyan su ka rubuta a bana.

Kara karanta wannan

EFCC ta 'gano' asusun da Sambo Dasuki ya tura kudin makamai

Rahotanni sun ce shugaban hukumar, Farfesa Ishaq Oloyede zai gana da manema labarai a babban birnin Tarayya Abuja ranar Litinin kan sakamakon jarrabawar da sauran batutuwa.

Hukumar JAMB na shirin bayyana sakamakon jarrabawar
Farfesa Ishaq Oloyede zai tattauna da manema labarai kan UTME Hoto: JAMB
Asali: Facebook

Rahoton Daily Trust ya bayyana cewa akwai alamu masu karfi na sakin sakamakon wasu a yau Litinin, yayin da za a saki na sauran bayan an yi mu su duba na tsanaki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

JAMB ta jinkirta fitar da sakamakon UTME

A bana an samu banbancin da sauran shekaru inda hukumar JAMB ke fitar da sakamakon UTME a kwana daya zuwa biyu bayan rubuta jarrabawar.

Hukumar a wannan shekarar ta ce za ta tsefe, ta tace jarrabawar domin tabbatar da cewa ba a yi satar amsa ba kafin ta saki sakamakon.

Dalibai sama da miliyan daya ne su ka rubuta jarrabawar a cibiyoyi 700 a fadin Najeriya, kamar yadda The Sun ta wallafa rahoto.

Kara karanta wannan

Yawan mutuwa: An fara zargin abin da ya haddasa mutuwa barkatai a Kano

JAMB: Dalibai za su rasa guraben karatu

A baya mun kawo mu ku yadda ake fargabar dalibai sama da miliyan daya za su rasa guraben karatu a manyan makarantun da ke kasar nan.

Ministan ilimi, Farfesa Tahir Mamman ne ya bayyana haka, wanda ke nufin dalibai miliyan 1.5 ba za su shiga manyan makarantu a bana ba.

Ministan ya shawarci iyayen yara su rika sa yaransu koyon sana'o'in hannu dokin gujewa shiga matsala sakamakon rasa guraben karatun.

Asali: Legit.ng

Online view pixel