Kwana Ya Kare: Fitacciyar Jarumar Kannywood da Ta Fito a Shirin Dadin Kowa Ta Rasu

Kwana Ya Kare: Fitacciyar Jarumar Kannywood da Ta Fito a Shirin Dadin Kowa Ta Rasu

  • Jarumar Kannywood da tauraruwarta ta haska a shirin fim mai dogon zango na Dadin Kowa, Jamila Gwarzo ta riga mu gidan gaskiya bayan gajeruwar jinya a Kano
  • Rahotanni sun nuna cewa jarumar ta rasu ne a gidanta da ke karamar hukumar Gwarzo ta jihar Kano kuma tuni aka yi jana'izarta a masallacin Juma'a
  • Abokin aikinta a Kannywood, Ali Rabiu Ali ya tabbatar da labarin rsuwar Jamila, tare da yin addu'ar Allah Ya gafarta mata, Ya yi mata rahama

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Jarumar masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Jamila Saleh Gwarzo ta riga mu gidan gaskiya bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.

Jaruma Jamila Gwarzo ta yi fice a fina-finan Hausa musamman rawar da ta taka a matsayin matar Dantani Mai Shayi a cikin shiri mai dogon zangi watau Dadin Kowa.

Kara karanta wannan

Wuta ta kama rigi rigi a fitacciyar kasuwa, an tafka asara mai yawa a jihar Kano

Jamila Gwarzo.
Jarumar masana'antar Kannywood, Jamila Gwarzo Hoto: Jamila Saleh Gwarzo
Source: Facebook

Jaruma Jamila Gwarzo ta rasu

Daya daga cikin jaruman Kannywood, Ali Rabiu Ali ya tabbatar fa rsuwar abokiyar aikin na sa a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook jiya Asabar, 5 ga watan Satumba, 2026.

Bayanai sun nuna cewa Jamila ta rasu ne bayan fama da ciwon ciki na dan lokaci a gidanta da ke karamar hukumar Gwarzo ta jihar Kano ranar Juma'a da ta gabata, 4 ga watan Satumba, 2026.

Jarumi Ali ya yi wa marigayiyar addu'ar neman samun rahama a wurin Allah SWT, tare da tuna ganawarsu ta karshe lokacin da ya je gaishe ta har gida.

Jarumi Ali ya tuna haduwarsu ta karshe

Ali ya bayyna cewa tuni aka yi jana'izarta a babban masallacin Juma'a na Gwarzo d ke jihar Kano kamar yadda addinin musulunci ya tanada.

Ya ce:

"Allah Ya jikanki Jamila Saleh Gwarzo! Abokiyar aikina shekara da shekaru ba mu taba sabawa ba, ranar Litinin na kira wayarta za ta hada ni da wani makocinta sai na ji muryarta kasa kasa, ta ce min bata da lafiya."

Kara karanta wannan

Bayanai sun fito da aka zargi Ahmad Gumi da dauke matar da wani ya auro daga Morocco

"Ina tashi na zarce gidansu na duba ta har na hada ta da uwargidana a waya suka gaisa ta yi mana Addu"'a, ashe ita ma tana bukatar Addu'a a nan kusa.
"A daren nan na ji labarin rasuwarta. Anyi Jana'izarta a babban masallacin Juma'a na garin Gwarzo. Allah Ya karbi shahadarta ya sada ta da Annabin Rahma sallAllahu alaiHi wasallam."

Jarumin Nollywood ta Najeriya ya rasu

A wani rahoton na daban, kun ji cewa jarumin masana'antar shirya fina-finai ta Nollywood, Solomon Akiyesi ya riga mu gidan gaskiya bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.

‘Yar marigayin ta bayyana cewa Akiyesi ya koka da ciwon kirji a daren kafin rasuwarsa, inda aka kai shi asibiti aka gano yana fama da gyambon ciki (ulcer) tare da ba shi magani.

Abokan aikinsa sun shiga shafukan sada zumunta suna alhinin rasuwarsa, suna bayyana shi a matsayin jarumi mai ƙwarewa wanda ya taka rawa a fina-finai da zai sa a rika tunawa da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262