An Yi Babban Rashi a Kannywood bayan Rasuwar Mahaifin jaruma, Rahama Sadau

An Yi Babban Rashi a Kannywood bayan Rasuwar Mahaifin jaruma, Rahama Sadau

  • Masana'antar Kannywood ta yi babban rashi bayan sanar da rasuwar mahaifin shahararriyar jarumar Kannywood
  • An tabbatar da mutuwar mahaifin jaruma, Rahama Sadau da safiyar yau Lahadi 22.ga watan Yunin 2025 da muke ciki
  • Majiyoyi suka ce marigayin ya rasu a jihar Kaduna, kamar yadda ta bayyana a wani saƙo da ga wallafa a kafar sadarwa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kaduna - An shiga cikin jimami a masana'antar Kannywood bayan sanar da rasuwar mahaifin daya daga cikin jarumanta.

Mahaifin fitacciyar jarumar Kannywood, Rahama Sadau, Alhaji Ibrahim Sadau, ya riga mu gidan gaskiya.

Mahaifin Rahama Sadau ya riga mu gidan gaskiya
An tabbatar da rasuwar mahaifin jaruma Rahama Sadau a Kaduna. Hoto: Rahama Sadau.
Asali: UGC

Jaruma Rahama Sadau ta yi rashin mahaifinta

Jaruma Rahama Sadau ita ta tabbatar da haka a yau Lahadi 22 ga watan Yunin 2025 a shafinta na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ce marigayin ya rasu a garin Kaduna kamar yadda majiyoyi suka tabbatar ranar Lahadi.

Jaruma Rahama Sadau ta bayyana hakan cewa 'Allah Ya yi wa mahaifina rasuwa…' sannan ta saka hoto da aka rubuta Inna lilLahi wa inna ilaiHi raji’un sau uku.

Mahaifin jaruma Rahama Sadau ya rasu a Kaduna
Ali Nuhu ya jajantawa Rahama Sadau bayan rashin mahaifinta. Hoto: Ali Nuhu Mohammed.
Asali: Facebook

Sakon jaje da Ali Nuhu ya wallafa a shafinsa

Shima abokin aikinta, Ali Nuhu, ya wallafa hoton jaruma Rahama Sadau da mahaifinta, yana mai tabbatar da rasuwar.

Ali Nuhu ya wallafa sanarwar a yau Lahadi 22 ga watan Yunin 2025 a shafinsa na Facebook inda ya yi mata ta'aziyya.

A karshe, ya roƙi Ubangiji y gafarta masa kura-kuransa da kuma ba iyalansa hakurin jure wannan babban rashi da suka yi na bango a cikin iyalinsu.

Ya ce:

"Innalillahi wa inna ilahir raj'un,
Allah ya yi wa Alhaji Ibrahim Sadau, mahaifin @rahamasadau rasuwa, Allah ya jikan shi da rahama, ya sa mutuwa hutu ne a gareshi.
"Muna rokon Allah ya bai wa iyalanshi da yan'uwa hakuri da juriyar rashin shi. Amin."

Rahama Sadau ta roki addu'a daga al'umma

An yi jana'izar marigayin Ibrahim Sadau, kamar yadda addinin Musulunci ya tanada a gidansa da ke Unguwar Rimi a Kaduna.

Rahama Sadau, wacce ta shahara a masana’antar Kannywood da kuma fina-finan Najeriya baki ɗaya, ta bayyana cewa rasuwar mahaifinta babban rashi ne da ba za a iya cike gibinsa ba.

Ta nemi addu'ar alheri daga al'umma don Allah ya gafarta wa mahaifinta, ya kuma ba su hakurin jure wannan babban rashi.

Marigayin Alhaji Ibrahim Sadau ya bar ƴaƴa mata da maza, ciki har da jarumar, kuma an bayyana shi a matsayin uba nagari, mai tausayi da kishin addini da al’umma.

An yi rashin malamin malamai a Kaduna

Mun ba ku labarin cewa Musulmi a Zaria da ke jihar Kaduna sun rasa babban malami, Sheikh Idris Adam Kumbashi, wanda ya rasu bayan fama da jinya.

An tabbatar da cewa Sheikh Kumbashi wanda ake kira Abu Sumayya, ya sadaukar da rayuwarsa wajen hidimar addini, da'awa da koyarwa lokacin da yake raye.

Majiyoyi sun ce an yi sallar jana’izarsa da misalin karfe 1:30 a masallacin Juma’an Dan Magaji da ke birnin Zaria a jihar Kaduna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.