An Yi Rashin Malamin Malamai: Fitaccen Shehin Musulunci a Zaria Ya Kwanta Dama

An Yi Rashin Malamin Malamai: Fitaccen Shehin Musulunci a Zaria Ya Kwanta Dama

  • Al’ummar Musulmi a Zaria sun rasa babban malami, Sheikh Idris Adam Kumbashi, wanda ya rasu bayan fama da jinya a jihar Kaduna
  • Sheikh Kumbashi wanda ake kira Abu Sumayya, ya sadaukar da rayuwarsa wajen hidimar addini, da'awa da koyarwa lokacin da yake raye
  • An tabbatar da mutuwarsa ne a dandalin Facebook, inda aka ce an yi jana’izarsa da misalin karfe 1:30 a masallacin Juma’an Dan Magaji

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Zaria, Kaduna - Al'ummar Musulmi sun yi babban rashi na wani fitaccen malamin Musulunci a jihar Kaduna.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa Sheikh Idris Adam Kumbashi ya riga mu gidan gaskiya a Zaria.

An rashin malamin Musulunci a Kaduna
Sheikh Idris Adam Kumbashi ya rasu a Zaria. Hoto: Idris Kumbashi.
Asali: Facebook

An yi rashin malamin Musulunci a Zaria

Shafin First Aid Group na Izalah a Zaria ya tabbatar da haka a manhajar Facebook a yau Asabar 21 ga watan Yunin 2025

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton ya ce marigayin da ake yi wa lakabi da Abu Sumayya ya rasu ne bayan fama da jinya.

An tabbatar da cewa marigayin Sheikh Kumbashi ya karar da rayuwarsa wurin hidima ga addini, da'awa karantarwa da sauransu.

Sanarwar ta ce:

"Cikin yanayi da jimami muke sanar da al'umma rasuwar babban malami Sheikh Idris Adam Kumbashi (Abu Sumayya).
"Malam ya karar da rayuwarsa wurin hidima ga addini, da'awa, karantarwa da sauransu.
"Muna addu'ar Allah Ta'alah ya ji kan malam ya gafarta masa ya yi masa rahama, Allah yasa aljannah ce makoma da dukkan Musulmi baki daya."
Malamin Musulunci ya rasu a Kaduna
An sanar da rasuwar Sheikh Idris Adam Kumbashi a Kaduna. Hoto: Legit.
Asali: Original

Yaushe aka gudanar da sallar jana'izar marigayin?

Majiyoyi da muka samu sun tabbatar da cewa an gudanar da jana'izarsa da misalin karfe 1:30 na rana a masallacin Juma'a na dan Magaji a Zaria.

Al'umma da dama sun yi jimamin rashin malamin addinin wanda suka ce ya yi kaurin suna wurin ilmantarwa da tarbiyyantar da al'umma.

Wani Ameer Auwal Sani ya tabbatar da mutuwar marigayin a shafin Facebook inda ya yi addu'ar Allah ya yi masa rahama ya sanya shi gidan aljanna.

Martanin mutane kan rashin malamin a Zaria

Mutane da dama sun tofa albarkacin bakinsu kan rashin da aka yi inda mafi yawansu ke addu'ar Ubangiji ya gafarta masa.

Najeeb T Bash:

"Allah ya jikanshi da rahama ya gafarta masa ameen ya rabbi."

Muhammad Abdullahi:

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Allahumma gafirlahu warhamhu."

Dalhatu Umar:

Allah ya jikanshi da rahama."

Muhammad Muneer Mikail:

"Allah ya sa can yafi mashi nan."

Marwan Ismail:

"Allah ya gafarta masa."

Ɗan Sheikh Argungu ya riga mu gidan gaskiya

Kun ji cewa Allah ya karbi ran Abdulmannan Abubakar Giro Argungu rasuwa a garin Argungu da ke Jihar Kebbi, bayan gajeruwar jinya.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa an gudanar da jana’izarsa ranar Asabar da karfe 2:00 na rana a Masallacin Idi na garin Argungu.

Malamai da dama sun nuna alhini kan rashin da aka yi ciki har da Sheikh Isa Ali Pantami wanda ya bayyana jimaminsa tare da fatan Allah ya saka masa da Aljanna.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.