'Bidiyon Batsa': Manyan Jarumai 2 da Aka Hana Su Fitowa a Finafinan Hausa a 2025
- Hukumar tace fina-finai ta Kano ta dakatar da wasu jarumai mata uku da kuma wani mawakin Kannywood a farkon shekarar nan
- Shugaban hukumar, Abba El-Mustapha, ya umarci kada a kara sanya jaruman a fim, ko a tace fina-finai ko waƙoƙin da suka fito a ciki
- Legit Hausa ta yi bayanin abin da ya jawo hukumar tace finafinan ta dakatar da Samha M Inuwa, Usman Soja Boy da wasu jarumai biyu
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Hukumar tace finafinai da dab'i ta jihar Kano ta dakatar da wasu fitattun 'yan Kannywood, ciki har da jaruma Samha M. Inuwa.
Wannan mataki ya biyo bayan zarge-zargen rashin da'a, fitar da tsiraici da kuma batsa da suka mamaye bidiyoyin da suke wallafawa a kafafen sada zumunta.

Asali: Instagram
Legit Hausa ta yi bayani kan jaruman da aka dakatar daga Kannywood a 2025:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Jaruma Samha M Inuwa
A ranar Asabar, 4 ga Janairun 2025, hukumar tace fina-finai da dab'i ta jihar Kano karkashin jagorancin Abba El-Mustapha ta dakatar da jaruma Samha M Inuwa.
Hukumar ta dakatar da jarumar na tsawon shekara daya bisa zarge-zargen sanya tufafin da ba su dace ba, kamar yadda rahotanni suka tabbatar.
Sanarwar da jami'in watsa labarai na hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman, ya fitar, ta bayyana cewa an dakatar da jarumar saboda nuna tsiraici da furta kalaman batsa a bidiyoyi.
Rahoton ya kara da cewa an sha gargaɗin jarumar game da irin tufafin da take sanyawa da kuma wasu kalaman rashin tarbiyya, amma ta yi kunnen uwar shegu.
Bidiyon da ake zargin ya jawo dakatarwar
Legit Hausa ta gano bidiyon da ake zargin ya jawowa jaruma Samha matsala, wanda ya sa hukumar ta yanke shawarar dakatar da ita.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Kano ta yafewa masu zanga zanga, an dakatar da shari'ar zargin cin amanar kasa
A cikin bidiyon, wanda aka wallafa a shafin mutan_kannywood na Instagram, an ga jarumar ta sanya kaya da ke bayyana surar jikinta sosai.
Wasu sun yi korafi cewa kayan sun matse jikinta, kuma hakan yana haifar da yanayi mai tayar da hankali ga masu kallo, musamman maza.
Kalli bidiyon a kasa:
2. Mawaki Usman Soja Boy
Hukumar tace fina-finai da dab'i ta jihar Kano ta ce ta samu korafe-korafe da dama kan mawaki Usman Soja Boy saboda yawaitar batsa a bidiyonsa.
Hakan ya sa hukumar ta dakatar da mawakin tare da wasu jarumai mata da suka fito a bidiyonsa na baya-bayan nan, kamar yadda muka ruwaito.
Sanarwar, wacce Abdullahi Sani Sulaiman ya fitar, ta tabbatar da cewa an kwace lasisin Soja Boy da wasu mata biyu daga Kannywood.
Shugaban hukumar, Abba El-Mustapha, ya bayar da umarni kada a kara tace fina-finai ko waƙoƙin da Soja Boy da matan suka fito a ciki.

Kara karanta wannan
Asiri ya tonu: Matasa sun yi tara tara, sun kama malamai 2 da wasu abubuwan ban mamaki
Me Soja Boy ya ce kan dakatarwar?
Da alama dakatarwar da aka yi wa Soja Boy ba za ta yi tasiri ba, domin ya ce ko kadan ba ta dame shi ba.
Mun ruwaito cewa, Soja Boy ya yi ikirarin shi ne yake taimakon masana'antar Kannywood, ba akasin haka ba, don haka dakatarwar ba ta taba shi ba.
"Ace an kore ni daga Kannywood abun ban dariya ne. Kannywood ba ta taba taimaka mini ba, ni ma na taimaka mata," inji Soja Boy.
Ya kara da cewa fina-finan Kannywood kamar su Na Ladidi da Yahoo Boy ne suka sa 'yan Arewa suka san shi, amma ya dade da yin suna a duniya.
Martanin furodusa kan kalaman Soja Boy
A kan batun cewa ba a taba biyansa kudin aiki ba, furodusan Kannywood, Abdulaziz Dan Small, ya karyata kalaman Soja Boy.
A zantawarsa da wakilin Legit Hausa, Dan Small ya ce:
"Ban so na yi magana a kan maganganun da ya yi ba, saboda ni akwai mutunci a tsakaninmu, amma tun da masana'antarmu ya taba, dole na gyara maganarsa.
"Kamar yadda na fada a baya, zan sake maimaitawa, ni nan na kamawa Soja Boy dakin otel har karo biyu, inda na kashe N300,000.
"Ka ga ba tun ya zo ya ce wai babu wanda ya taba kama masa otel ba ta taso ba. Kuma na biya kara masa da N50,000 a wannan aikin, duk don na mutunta shi."
Abdulaziz Dan Small ya yi kira ga masu shirya fina-finai da su dauki wannan a matsayin darasi, su rika biyan wadanda suka gayyato aiki don gudun gori wata rana.
Wasu jarumai mata da aka dakatar
Baya ga Soja Boy da Samha M Inuwa, hukumar ta dakatar da wasu jarumai mata biyu da suka fito a bidiyonsa.
Sanarwar hukumar ta nuna cewa matan sun yi bidiyo da ke dauke da ababen da suka saba dokokin tace fina-finai.
Sai dai har yanzu ba a samu cikakken bayani kan wadannan jarumai mata biyu ba, amma karin rahoto zai zo nan gaba.
"A cire Firdausi daga Jamilun Jidda" - 'Yan kallo
A wani labarin, mun ruwaito cewa masu kallon shirin Jamilun Jidda sun yi kira da a sauya Firdausi Yahaya tare da maye gurbinta da Humaira a matsayin diyar Farfesa Inde.
Sun roki mai shirya shirin, Abubakar Bashir Maishadda, da ya dauki wannan mataki idan har yana son shirin ya ci gaba da nishadantar da masu kallo.
Asali: Legit.ng