Ni Ba Dan Daba Bane Amma Na Taba Rashin Ji – Sadiq Sani Sadiq

Ni Ba Dan Daba Bane Amma Na Taba Rashin Ji – Sadiq Sani Sadiq

  • Jarumin masana'antar Kannywood, Sadiq Sani Sadiq, ya nesanta kansa daga rade-radin da ake yi na cewar shi dan daba ne a baya
  • Sadiq wanda aka fi sani da Gambo uban Tani ya ce shi dai ya yi farauta a lokacin da yake tasowa
  • Jarumin fim din ya ce duk da rashin jin da ya yi, Allah bai kaddare shi da yin shaye-shaye ba

Shahararren jarumin masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Sadiq Sani Sadiq ya karyata rade-radin cewa shi dan daba ne a baya.

Da yake amsa tambayoyi a shirin "Gabon's Room Talk Show' wanda jaruma Hadiza Aliyu Gabon ke gabatarwa a Youtube, jarumin ya ce shi mafaruci ne a lokacin da yake tasowa.

Sadiq ya ce ya taba yin farauta
Ni Ba Dan Daba Bane Amma Na Taba Rashin Ji – Sadiq Sani Sadiq Hoto: Manuniya
Asali: UGC

Na siyar da mai na bunburutu, Jarumi Sadiq Sani Sadiq

Kara karanta wannan

"Ina Sa Rai Sanadiyar Kannywood Zan Samu Gidan Aljannah", Inji Sadiq Sani Sadiq

Ya ce shakka babu ya dan taba rashin ji da yake tasowa domin har ya yi sana'ar siyar da mai na bunburutu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai ya ce duk da kasancewarsa dan bunburutu bai taba yin shaye-shaye ba amma dai fada ko dambe bata yi masa wahala a lokacin.

Ya ce:

"Mutane ne basa bambancewa, akwai dan daba, akwai mafarauci. Ni mafarauci ne, na yi farauta a lokacin da nake ganiyar kuruciya da kuma rashin ji. Na yi farauta, na dan taba farauta gefe-gefe haka sannan kuma na siyar da mai irin na jarka-jarka 'black market' kuma yawancin wanda ya yi wannan sana'ar za a gan shi ba shi da tsoro. Toh ni ba dan daba bane amma ni mafarauci ne ko yanzu dama ta samu idan na samu nutsuwa ta wani gefen na kan yi harbi in fasa in yi ciki.

Kara karanta wannan

Mista Ibu: Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki Ya Dauki Nauyin Asibitin Jarumin Da Ke Jinya

"Rashin ji da na yi a harkar farauta da na yi, kin san akasari a cikin kashi dari, kashi tamanin na mafarauta suna da fushi saboda wasu dan abubuwa da ake amfani da su, za ka ji kai kadai kana zaune musamman idan aka dan kada wani gangan za ki ji ka soma tsuma.
"Abun fada baya yi mun wuya a da, yanzun nan sai in tube riga mu daku da ke ba damuwa bane. Sai ni ban yi shaye-shaye ba inda Allah ya taimake ni kenan, duk rashin jin da na yi Allah bai kaddaramun shaye-shaye ba, shima kuma saboda addu'an iyaye ne."

Ina fatan fim ya yi sanadiyar shigata Aljannah, Sadiq Sani Sadiq

A baya, mun ji cewa jarumin fim Sadiq Sani Sadiq wanda aka fi sani da 'Gambo uban Tani', ya bayyana cewa yana fatan fim ta zama silar shigarsa gidan Aljanna.

Sadiq ya bayyana hakan ne yayin da ya fito a shirin abokinyar sana'arsa jaruma Hadiza Aliyu Gabon mai taken ‘Gabon's Room Talk Show’ wanda take gabatarwa a shafin Youtube.

Asali: Legit.ng

Online view pixel