Ba zan daina cashewa a fim ba - Sadiq Sani Sadiq

Ba zan daina cashewa a fim ba - Sadiq Sani Sadiq

Fitaccen jarumin Kannywood, Sadiq Sani Sadiq ya bayyana cewa ba zai daina rawa ba a fina-finan Hausa har sai ya tsufa kuma baya iya rawan. Sadiq ya sanar da hakan ne a wata hira da yayi da BBC Hausa a ranar Laraba.

Sadiq ya ce ba zai daina rawa ba a fim "ba nan kusa ba saboda inason cashewa. Koda kuwa na tsufa zan kada kafafu na".

Sadiq na daga cikin 'yan Kannywood da ke jan zarensu a masana'antar fim din. Ana ganin hazakarsa da kuma kwarewarsa ta yadda yake iya taka kowacce rawa da aka bashi a fim.

Ana jinjinawa iya rawarsa duk da yana biye da jarumi Adam Zango ne wanda ba a iya rawa kadai ya tsaya ba, har kamfanin kida da waka mai suna WhiteHouse Racords gareshi.

Ba zan daina cashewa a fim ba - Sadiq Sani Sadiq
Ba zan daina cashewa a fim ba - Sadiq Sani Sadiq
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Ba mu maraba da kai a jam'iyyar mu: APC ta fadawa tsohon gwamnan PDP

Sadiq ya taka rawar gani a manyan fina-finai da suka yi suna wadanda suka hada da Dan Marayan Zaki, Ali Ya ga Ali, Hanyar Kano, Wani Gari, Mati da Lado da kuma fim din da ke tashe mai suna Mati A Zazzau.

"Ina ganin matukar ina a matsayin jarumi a Kannywood, zan ci gaba da rawa har sai na tsufa," ya ce.

Sadiq ya kara da bayyana cewa bashi da niyyar kara aure. "Ina kaunar matata kuma ita kadai gareni. Ina da kawaye kuma wasu a Kannywood suke," ya ce.

A lokacin da aka tambayeshi waye babban abokin shi, sai yace Rahama Sadau. "Rahama Sadau na da matukar muhimmanci a gareni. Mace ce mai karfin hali, mai gaskiya kuma akwai alkawari," ya ce.

A yayin bayyana abinda ke tunzurashi nan da nan, jarumin ya ce gulma ce. "Na tsani a yi maganar wani ko wasu mutane a gabana. Hakan na bata min rai ba kadan ba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel