Ina Fatan Fim Ya Zama Silar Shigata Gidan Aljanna, Inji Sadiq Sani Sadiq

Ina Fatan Fim Ya Zama Silar Shigata Gidan Aljanna, Inji Sadiq Sani Sadiq

  • Shahararren jarumin Kannywood, Sadi Sani Sadiq ya yi wasu zantuka masu tsuma zukata kan sana'arsa ta fim
  • Jarumin fim din ya ce yana fatan wannan sana'a tasa da yake yi za ta yi sanadiyar shigarsa gidan Aljannah
  • Sadiq ya kuma bayyana cewa bai da ubangida a harkar fim amma akwai wasu da yake ganin girman su

Fitaccen jarumin masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Sadiq Sani Sadiq, wanda aka fi sani da 'Gambo uban Tani', ya bayyana cewa yana fatan fim ta zama silar shigarsa gidan Aljanna.

Sadiq ya bayyana hakan ne yayin da ya fito a shirin abokinyar sana'arsa jaruma Hadiza Aliyu Gabon mai taken ‘Gabon's Room Talk Show’ wanda take gabatarwa a shafin Youtube.

Sadiq Sani Sadiq ya ce yana burin fim ya yi sanadiyar shigarsa al'jannah
Ina Fatan Fim Ya Zama Silar Shigata Gidan Aljanna, Inji Sadiq Sani Sadiq Hoto: Alummar Hausa
Asali: UGC

Jarumin ya bayyana cewa ya shigo harkar fim ne ba tare da ubangida ba domin a cewarsa babu wanda ya koya masa yadda ake fim.

Kara karanta wannan

Reno Omokri Ya Yi Martani Yayin da Sheikh Gumi Ya Caccaki Wike Kan Hada Kai Da Isra’ila

Sai dai ya ce yana ganin mutane biyar da suka hada da Bello Muhammad Bello, Ali Nuhu, Adam Zango, Aminu Saira, Umar UK.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kannywood ya zamar da ni mutum a lokacin da ban san ina zani ba - Sadiq Sani

Da yake bayani kan rawar ganin da Kannywood ta taka a rayuwarsa, jarumin ya ce masana'antar fim din ta mayar da shi mutum a lokacin da yake wangalili bai ma san inda ya nufa ba.

Ya ce:

"Kannywood ta mayar da ni mutum a lokacin da nake bindin-bindin ban ma san ina na nufa ba, Kannywood ta yi mun sutura, ta yi mun riga da wando. Kannywood ta yi mani komai da komai. Ina ma sa rai sanadiyar Kannywood In shaa Allahu zan samu gidan aljannah."

Da yake bayyana dalilinsa na cewa fim zai kai shi aljannah, jarumin ya ce ya yarda sana'a yake yi.

Kara karanta wannan

Za Su Kashe Ni – Abokin Fadan Kwankwaso a NNPP Ya Ce Ya Na Fuskantar Barazana

Ya kuma ce a cikin kowace irin sana'a koda malumta ne na koyar da yara ilimin addini, mutum na iya samun wuta, yana iya samun aljannah cewa ya danganta da yadda mutum ya tafiyar da sanar ne.

Ya ci gaba da cewar:

"Na yarda sana'a ce nake yi kuma a harkar fim na yarda dari bisa dari daidai gwargwado ina ba ma addinina gudunmawa da al'adata. Ina kuma sa rai idan Allah ya yarda, in shaa Allahu zan tashi ranar gobe kiyama a gaban Ubangijina da kyakkyawar fuska da kyakkyawan sakamako ta yadda na gudanar da sana'ata."

Bukola Saraki ya dauki nauyin asibitin jarumin fim da ke jinya

A wani labarin kuma, mun ji cewa gidauniyar Abubakar Bukola Saraki ta biya dukkanin kudaden asibitin shahararren jarumin Nollywood, John Okafor, wanda aka fi sani da Mista Ibu.

An bayyana wannan labarin ne a cikin wata sanarwa da aka fitar a shafin gidauniyar na Facebook a ranar Juma'a, 20 ga watan Oktoba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel