Kotu ta yi umarnin damko jarumi Sadiq Sani Sadiq kan zargin almundahana

Kotu ta yi umarnin damko jarumi Sadiq Sani Sadiq kan zargin almundahana

  • Alkali Sagir Adamu na wata kotun Musulunci da ke zama a Hotoro masallaci ya bukaci dan sandan kotu ya cafko masa jarumin kannywood Sadiq Sani Sadiq
  • Wani mashiryin fim mai suna Aliyu Adamu Hanas ne ya maka shi a kotun sakamakon karbar kudi har dubu tamanin amma ya ki halartar shirya fim kuma ya ki biyan sa
  • Kotu ta aike wa jarumin da sammaci amma ba a same sa ba, ta umarci a manna a gidansa kuma ya ki zuwa kotun, lamarin da ya tunzura alkali ya umarci a kama shi

Kano - Wata kotu mai zama a jihar Kano ta bai wa dan sandan kotu umarnin cafko mata fitaccen jarumin masana'antar Kannywood, Sadiq Sani Sadiq.

Kara karanta wannan

Dillalin gidaje ya mutu a dakin Otal bayan shakatawa da matar aure

Alkali Sagir Adamu na kotun shari'ar Musulunci mai zama a Hotoro masallaci ne ya bayar da umarnin damke jarumin saboda bijirewa umarnin kotun, Freedom Radio ta ruwaito.

Kotu ta yi umarnin damko jarumi Sadiq Sani Sadiq kan zargin almundahana
Kotu ta yi umarnin damko jarumi Sadiq Sani Sadiq kan zargin almundahana. Hoto daga @sadiqsanisadiq
Asali: Instagram

Tun farko dai, wani mashiryin fina-finai mai suna Aliyu Adamu Hanas ya kai karar jarumin saboda ya bashi kafin alkalami na kudi domin za su fara aikin shirya wani fim, sai dai jarumin ya ki yin aikin.

Bayan nan, Aliyu Adamu Hanas ya yi kokarin karbar kudinsa, amma jarumin ya hana shi, lamarin da ya sa ya gaggauta garzayawa gaban kotu domin neman gumin sa.

Daga nan kotu ta aika wa jarumi Sadiq da sammaci amma sai ba a same shi a gida ba, alkali ya umarci a manna masa takardar sammacin a kofar gidan sa da ke Tudun Yola amma kuma ya ki bayyana a gaban kotun.

Kara karanta wannan

Rikici kan Kayan Mata: Kotu ta bayar da belin Jaruma mai Kayan Mata

Freedom Radio ta ruwaito cewa, wanda ke neman hakkin sa ya na bukatar kudin sa har dubu tamanin ne daga wurin jarumi Sadiq Sani Sadiq.

Daga bisani zai maka karar jarumin a gaban kotu kan zargin bata masa lokaci da ya yi da kuma janyo masa tafka mummunar asara kan kin halartar shirin fim din.

Bidiyon mace mai tsayin farce inci 12 wanda ta shekara 30 ta na tarawa, ta sanar da yadda ta ke girki

A wani labari na daban, Cordelia mace ce mai shekaru 59 a duniya kuma hanyar bayyana kanta na farko shi ne farcen ta da suka kai tsayin inci 12.

Mazauniyar yankin Virginia din a Amurka ta zama abun kallo a manhajar TikTok ana tsaka da annobar korona yayin da ta wallafa bidiyon ta tana wanke farcen, APost ta ruwaito.

A yayin da Hooked on The Look suke tattaunawa da ita, Cordelia ta bayyana cewa ta fara sha'awar tara farce ne bayan da mahaifiyar ta tara wanda ya fi wannan tsayi.

Kara karanta wannan

Rayuwar Aure: Kotu ta datse Igiyoyin auren wata mata saboda mijin ya faɗa soyayya da kare

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: