Fitaccen Jarumin Kannywood Abdullahi Karkuzu Ya Nemi a Taimaka Ma Sa Bayan Makanta Ta Same Shi

Fitaccen Jarumin Kannywood Abdullahi Karkuzu Ya Nemi a Taimaka Ma Sa Bayan Makanta Ta Same Shi

  • Shahararren jarumin fina-finan Hausa, Abdullahi Karkuzu ya nemi taimakon al'ummar Najeriya
  • Jarumi Karkuzu ya nemi taimakon ne saboda jarabawa ta makanta da ya tsinci kansa a ciki
  • Ya ce a yanzu haka ba ya da muhalli na kansa kuma ba shi da abinda zai ciyar da iyalinsa

Fitaccen jarumin fina-finan Hausa na masana'antar Kannywood Abdullahi Shuaibu wanda aka fi sani da Abdullahi Karkuzu, ya haɗu da jarabawa ta makanta, da yake ci gaba da fama da ita a yanzu haka.

A wani bidiyo da aka wallafa a shafin Zinariya da ke Facebook, jarumin ya bayyana irin halin da yake ciki.

Jarumin fim din Hausa ya makance, yana neman taimako
Jarumin fim Abdullahi Karkuzu ya nemi a taimaka ma sa. Hoto: Zinariya
Asali: Facebook

Idanun jarumin sun makance, ba za su ƙara gani ba

Karkuzu ya bayyana cewa ya sha fama wajen neman maganin idanunsa, inda daga bisani likitoci suka shaida ma sa cewa ba zai ƙara gani ba har abada.

Kara karanta wannan

Matar Aure Ta Kadu Yayin da Ta Isa Wajen Bikin Mijinta, Aminiyarta Ce Amaryar Da Ya Yi

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ce ya shafe shekaru aƙalla 40 yana wasan kwaikwayo, amma har yanzu ba ya da koda ɗaki, ballantana a ce ya mallaki gidan kansa.

Ya ƙara da cewa yanzu haka maganar da ake yi, gidan da yake zaune na haya ne, kuma an sanya shi kasuwa ana jiran mai saye.

Karkuzu ya kuma bayyana cewa da yawa daga cikin waɗanda suka fara sana'ar fim tare da su duk sun riga mu gidan gaskiya.

Jarumi Karkuzu ya nemi taimakon al'ummar Najeriya baki ɗaya

Abdullahi Karkuzu ya kuma bayyana cewa yana da mata da 'ya'ya da yake ɗaukar dawainiyarsu duk da wannan hali da ya tsinci kansa a ciki.

Ya yi kira ga ɗaukacin al'ummar Najeriya da su kawo ma sa ɗauki su taimaka ma sa ya mallaki muhallinsa na kansa.

Kara karanta wannan

‘Yadda Cire Tallafin Man Fetur Ya Tunzura Ni Aikata Fashi Da Makami’, Direba Ya Yi Bayani

Sannan ya kuma buƙaci a taimaka ma sa da ɗan abinda zai riƙe a hannu domin ya ci gaba da kula da iyalinsa.

Mutane da dama sun nuna alhininsu bisa wannan jarabawa da ta samu tsohon jarumin a cikin bidiyon da aka wallafa.

Jarumin Fim ya bayyana yadda barasa ta kusa janyo ma sa tafiya lahira

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan jarumin fina-finan kudancin Najeriya, Pete Edochie da ya bayyana yadda shan barasa ya kusa janyo ma sa halaka.

Jarumin ya bayyana cewa ya hau motarsa bayan ƙyanƙyamar barasa da nufin ya je wani wuri, sai dai ya ɓuge da bugawa wata babbar mota saboda hali na maye da yake ciki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel