Matar Aure Ta Kadu Yayin da Ta Isa Wajen Bikin Mijinta, Aminiyarta Ce Amaryar Da Ya Yi

Matar Aure Ta Kadu Yayin da Ta Isa Wajen Bikin Mijinta, Aminiyarta Ce Amaryar Da Ya Yi

  • Wani bidiyo da ya yadu ya nuna wata yar dirama da aka sha a wajen wani shagalin biki bayan matar ta gano cewa aminiyarta ce amaryar da mijinta ya yi
  • Ta tunkari matar cike da dacin rai da radadi a muryarta sannan ta hana mijinta ya taba ta
  • Jama'a sun yi martani kan lamarin yayin da mutane suka magantu a kan illar kawaye

An sha yar dirama a wajen wani shagalin biki lokaci da wata mata ta gano cewa mijinta na auren aminiyarta ne.

Lamarin da aka yada a dandalin soshiyal midiya, ya nuno matar tana fuskantar aminiyar tata cike da radadi a muryarta.

Ango ya ci amanar matarsa
Matar Aure Ta Kadu Yayin da Ta Isa Wajen Bikin Mijinta, Aminiyarta Ce Amaryar Da Ya Yi Hoto: @remedyblog
Asali: Instagram

Wani mutum mai suna, @priestagramm, wanda ya yi martani ga bidiyon, ya yi bayanin bacin ran matar inda ya bayyana cewa Wolof suke yi, wani yaren kasar Senegal ko Gambiya.

Kara karanta wannan

‘Yadda Cire Tallafin Man Fetur Ya Tunzura Ni Aikata Fashi Da Makami’, Direba Ya Yi Bayani

A cewarsa, matar ta zargi aminiyarta da munafurci mafi girma sannan ta kalubalanceta da ta kalleta a cikin ido sannan ta tabbatar mata da gaske auren za ta yi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Daga nan sai matar ta fada ma mijinta, angon, cewa ba da shi take magana ba. @priestagramm ya yi bayani kamar haka:

"Fassara - Dukkanku munafukai ne. Kada wanda ya taba ni a cikinku...Nabou kece babbar munafuka a cikin dukkanku...Ni za ki yi wa haka? Kin kasance kawata muddin rayuwa...Ki kalli cikin idanuna sannan ki fada mani "Ni na aikata maki wannnan"...Kafin ta fada ma mijinta cewa ba da shi take magana ba....Suna yaren Wolof ne, Yaren (senegal/Gambiya)."

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

omabarbie1 ta ce:

"Kawaye sun fi kowa yin abun da mai dace ba yanzu kuma iya karancin kawaye iya karancin dirama, kawaye sun gasa mun aya a hannu kuma har yanzu suna kan gasawa."

Kara karanta wannan

"Na Tausaya Mata": Matar Aure Ta Je Wurin Biki Ta Tarar Babbar Kawarta Mijinta Yake Aure, Bidiyon Ya Dauki Hankula

sheischidubem ta ce:

"Ya kamata mata su koyi dabi'ar gujema kawaye ko duk wanda ke son abun da suka mallaka, mai shi na iya kasancewa kawar kirki amma samun irin wannan dabi'ar babban kalubale ne."

lagosmealprepsociety ta ce:

"Na so yadda ta yi kwalliya sannan ta hadu don zuwa ta fuskance su. Ina hasashen abun da ke yawo a zuciyarta yayin da take zana giranta da fesa turare. Wannan rayuwar dai."

Yadda abokan ango suka nishadantar da mahalarta biki, sun tabbatar komai ya ji zam a tattare da shi

A wani labari na daban, wasu abokan ango sun kayatar da jama'ar da suka taru domin taya abokinsu farin ciki a ranar aurensa.

Abokan angon sun tabbatar da komai ya ji zam tun daga haduwar ango har zuwa yanayin shigarsa kafin suka bari ya isa ga amaryarsa don manna mata 'kiss'.

Asali: Legit.ng

Online view pixel