Za'a fara gabatar da wani kayattacen wasan kwaikwayo kan yaki da rashawa cikin harshen hausa

Za'a fara gabatar da wani kayattacen wasan kwaikwayo kan yaki da rashawa cikin harshen hausa

- An kashe naira miliyan 30 don hada wasan kwaikwayon da a ka yi kan yaki da cin hanci da rashawa

- An yi shi ne a harshen Hausa, za a kuma gabatar da shi ne a gidajen rediyo 8 a Arewacin Kasar nan

- Wasan na da fitowa guda156 wanda za a fara gabatarwa daga makon farko na watan Fabrairu 2018 har zuwa 2020

Nan ba da dadewa ba za a fara gabatar da wasan kwaikwayo a kan yaki da cin hanci da rashawa a tashoshin rediyo 8 da ke Arewacin Najeriya. An yi wasan kwaikwayon ne da harshen Hausa a inda a ka kashe kudi naira miliyan 30 don shirya shi.

Wasan kwaikwayo na N30m da harshen Hausa a kan yaki da rashawa na nan tafe
Wasan kwaikwayo na N30m da harshen Hausa a kan yaki da rashawa na nan tafe

Ciyaman din Kwamitin Amintattu na Kungiyar 'Yan Wasan Kwaikwayo na Najeriya (MOPPAN), mai suna Alhaji Abdulkarim Mohammed, shi ne ya tsara kuma ya shirya wasan wanda a ka sa wa suna Shugabanci.

KU KARANTA: An bijiro da rikicin makiyaya da manoma ne don raba kan Arewa - Ango Abdullahi

Mohammed ya bayyana cewar an shirya wasan ne don bayar da tallafi wurin yaki da rashawa a Kasar nan. Ma'aikatar Tallafi mai zaman kan ta, McArthur Foundation, ita ce ta dauki nauyin shirin.

Wasan ya na dauke ne da fitowa guda 156 wanda za a fara gabatarwa daga makon farko na watan Fabrairu na 2018 zuwa watan Fabrairu na 2020. Wasan kuma ya kunshi 'yan wasa 22 ne wadanda a ka zabo su daga mutane 88 da su ka nemi fitowa.

Mohammed ya bayyana cewar wannan wasa shi ne irin sa na farko. An kuma yi amfani da na'urori gangariya wurin daukar sa. An kuma yi sa ne a waje, wurare daban daban da su ka danganci shirin ba a dakin daukan shirye-shirye ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164