Mawaki Sufin Zamani Zai Saki Bidiyo Da Murya Na Neman Afuwar Matan Kannywood

Mawaki Sufin Zamani Zai Saki Bidiyo Da Murya Na Neman Afuwar Matan Kannywood

  • Hukumar yan sandan farin kaya DSS ta umurci mawaki Sarfilu Umar Zarewa (Sufin Zamani) ya yi bidiyo da murya na neman afuwar matan Kannywood
  • Hakan na zuwa ne bayan korafinsa da matan Kannywood suka yi wurin kungiyar MOPPAN kan wakar da ya fitar mai taken 'Matan Fim Ba Su Zaman Aure'
  • Matan na Kannywood sun ce wakar 'cin mutunci' ne a garesu hakan yasa DSS din ta umurci Sufin Zamani ya sake wata wakar kishiyan ta biya ya kuma rubuta takardar alkawarin cewa ba zai sake ba

Jami'an hukumar yan sandan farin kaya, DSS, sun kama mawakin Hausa, Sarfilu Umar Zarewa wanda aka fi sani da Sufin Zamani, rahoton Daily Trust.

Kungiyar masu fina-finai ta MOPPAN ce ta yi korafi kansa saboda wata waka da ya yi mai suna "Matan Fim Ba Su Zaman Aure."

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Yan Bindiga Sun Tafi Har Gida Sun Sace Matar Ciyaman Din NULGE Na Jihar Zamfara Da Cikin Wata 9

Sufin Zamani.
Mawaki Sufin Zamani Zai Yi Saki Bidiyo Da Murya Na Neman Afuwar Matan Kannywood. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Matan Kannywood ba su ji dadin wakar da Sufin Zamanin ya yi ba inda suka ce cin mutunci ne a gare su.

Hakan na cikin sanarwar da sakataren MOPPAN na kasa, Al-Amin Ciroma ya fitar.

Matan Kannywood sun rubuta wasikar korafi sun ce a bi musu hakkinsu

A cewar sanarwar, an dauki matakin ne sakamakon korafi da matan Kannywood suka yi cikin wasikar da Wasila Ismail ta rubuta a madadin matan.

Sun nemi shugabannin kungiyar su bi musu hakkinsu kan wakar da Sufin Zamani ya yi, wanda suke ganin kalaman cin mutunci ne gare su.

Sanarwar ta kara da cewa saboda korafin, shugaban MOPPAN na kasa, Dr Ahmad Saraki ya bada umurnin a gudanar da bincike bayan hakan ya rubuta wa DSS wasika yana neman su shiga tsakani.

Kara karanta wannan

Mun Baka Awa 48: PDP Za Ta Yi Wa Obasanjo Fallasa Idan Bai Yi Karin Haske Kan Maganan Da Ya Yi Kan Atiku Ba

Ta kuma ce an gayyaci mawakin bayan kammala bincike, an bukaci ya janye wakar mai taken 'Matan Fim Ba Su Zaman Aure.'

A cewar sanarwa, an bukaci mawakin ya yi bidiyo da murya ya nemi afuwa daga wurin matan.

An kuma umurci mawakin ya yi sabuwar waka kishiyan wakar ta farko sannan ya rubuta wasikar alkawarin ba zai sake sakin irin wakar ba da wasu abubuwan.

Mawakin, Sufin Zamani ya yi fice ne bayan sakin wakarsa ta farko, Yar Lukuta, kuma ya fara harka da Kannywood. Mawakin wanda aka haifa a Kaduna ya samu karbuwa saboda basirar da ya ke da shi na iya rera waka kan abubuwa da dama.

Ina Buƙatar Mijin Aure Cikin Gaggawa, In Ji Jarumar Fina-Finai Ta Najeriya

A wani rahoton, Gogaggiyar jarumar fina-fina ta Nollywood a Najeriya wacce aka dade ana damawa da ita, Eucharia Anunobi, ta ce neman mijin aure ta ke yi cikin gaggawa, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Shehu Sani: Idan An Kasa Nuna Makarantun da Tinubu ya Halarta, An ga Wadanda Ya Gina

A wata tattaunawa da BBC Ibo ta yi da ita, ta ce tana neman namijin da zai sanya mata zoben aure a yatsan ta.

Jarumar mai shekaru 56 ta ce tana fatan samun cikakken namiji, wanda ya ke da duk abinda mace ta ke nema a wurin mijin aure.

Asali: Legit.ng

Online view pixel