Da Dumi-Dumi: Yan Bindiga Sun Tafi Har Gida Sun Sace Matar Ciyaman Din NULGE Na Jihar Zamfara Da Cikin Wata 9

Da Dumi-Dumi: Yan Bindiga Sun Tafi Har Gida Sun Sace Matar Ciyaman Din NULGE Na Jihar Zamfara Da Cikin Wata 9

Zamfara - Yan bindiga sun sace matar shugaban kungiyar ma'aikatan kananan hukumomi, NULGE, ta Jihar Zamfara, Sanusi Mohammed Gusau.

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Matar, Ramatu Yunusa, wacce ke da ciki na wata tara, an sace ta ne a gidan mijinta da ke Damba a Gusau, safiyar ranar Talata.

Taswirar Jihar Zamfara.
Yan Bindiga Sun Sace Matar Shugaban NULGE Na Zamfara Da Ciki Na Wata 9. Hoto: @MobilePunch.
Asali: UGC

Da ya ke magana da The Punch, Gusau ya ce yan bindigan sun kutsa gidansa misalin karfe 1 na daren Talata sun sace matarsa mai juna biyu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ce, idonsa biyu lokacin da yan bindigan suka hauro katanga da nufin su sace shi amma sai ya boye inda ba za su ganshi ba.

"Sun hauro katanga kuma suka balle kofa na amma kafin su shigo dakin, na boye a wani wuri.

Kara karanta wannan

Cikakken jerin Sanatoci 58 da aka zazzage, ba za su koma kujerunsu a Majalisar Dattawa ba

"Da suka bincika gidan ba su gan ni ba, suka sace matata mai juna biyu, Ramatu," in ji shi.

Shugaban na NULGE ya ce matarsa na iya haihuwa a kowanne lokaci daga yanzu.

"Za ta iya haihuwa a kowanne lokaci yanzu domin a wannan makon ake sa ran za ta haihu."

Amma, ya ce har yanzu yan bindigan ba su tuntube shi ba.

Ba a samu ji ta bakin mai magana da yawun yan sandan Jihar Zamfara, SP Mohammed Shehu ba a lokacin hada wannan rahoton.

Jihar Zamfara Za Ta Fara Yanke Wa Masu Garkuwa Da Yan Bindiga Hukuncin Kisa

A bangare guda, Abdullahi Shinkafi, mashawarci na musamman kan harkoki tsakanin hukumomin gwamnati ga gwamnan Zamfara, ya ce Majalisar Dokokin Jihar ta amince da kudin dokar hukuncin kisa ga yan bindiga, rahoton The Cable.

"Yau, gwamna zai rattaba hannu kan dokar hukuncin kisa ga masu garkuwa, masu kai musu bayanai da sauran laifuka masu alaka da yan bindiga," in ji shi.

Kara karanta wannan

Rikicin kujerar Sanata Ahmad Lawan, ya dauki zafi, Machina ya yi wa Shugaban APC raddi

"Majalisar dokokin jihar, a jiya a Zamfara ta amince da dokar hukuncin kisa ga masu garkuwa da mutane, masu kai musu bayanai da masu basu gudunmawa."

Asali: Legit.ng

Online view pixel