Ina Buƙatar Mijin Aure Cikin Gaggawa, In Ji Jarumar Fina-Finai Ta Najeriya

Ina Buƙatar Mijin Aure Cikin Gaggawa, In Ji Jarumar Fina-Finai Ta Najeriya

  • Gogaggiyar jarumar fina-finan Nollywood, Eucharia Anubobi, ta ce tana neman mijin da zai aure ta cikin gaggawa
  • Ta bayyana hakan ne a wata tattaunawa da BBC Ibo ta yi da ita, inda jarumar mai shekaru 56 ta ce tana bukatar ta yi aure
  • A cewarta, ta na bukatar namiji mai kyawun suffa da kuma tsoron Ubangiji kuma kada ya kasance mai wata nakasa a tattare da shi

Gogaggiyar jarumar fina-fina ta Nollywood a Najeriya wacce aka dade ana damawa da ita, Eucharia Anunobi, ta ce neman mijin aure ta ke yi cikin gaggawa, Daily Trust ta ruwaito.

A wata tattaunawa da BBC Ibo ta yi da ita, ta ce tana neman namijin da zai sanya mata zoben aure a yatsan ta.

Ina Buƙatar Mijin Aure Cikin Gaggawa, In Ji Jarumar Fina-Finai Ta Najeriya
Ina Buƙatar Mijin Aure Cikin Gaggawa, In Ji Jarumar Eucharia Anubobi. Hoto: Daily Trust.
Asali: UGC

Jarumar mai shekaru 56 ta ce tana fatan samun cikakken namiji, wanda ya ke da duk abinda mace ta ke nema a wurin mijin aure.

Kara karanta wannan

Ina tsananin bukatar aure cikin gaggawa, Wata Jarumar masana'antar Fim a Najeriya ta cire kunya

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ta ce tana son namiji kyakkyawa mai tsoron Ubangiji

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito ta furta cewa:

“Don Allah, ina son yin amfani da wannan damar in sanar da duniya cewa ina son in yi aure cikin gaggawa. Don haka kasaitaccen namiji ya bayyana kansa kuma ya sanya min zobe a hannuna. Abin da nake so tattare da shi shi ne ya kasance mai tsoron Ubangiji kuma kyakkyawa.
“Wajibi ne ya cancanta, ya kuma mallaki duk wani abu da ake so a wurin namiji. Kada ya kasance mai wata nakasa, shikenan abin da zan ce.”

Haifaffiyar Jihar Imo ce

An zargi jarumar wacce ta koma fasto da soyayya da abokin sana’arta, Lucky Oparah, wanda ta musanta.

Asalinta haifaffiyar Owerri ce, Jihar Imo kuma bayan ta kammala karatunta na sakandare ta zarce Cibiyar Gudanarwa ta Fasaha (IMT), Enugu, inda ta yi karatun diploma a fannin jaridanci.

Kara karanta wannan

Wani Bawan Allah ya maida G-Wagon ta zama gingimari, ta dawo motar dakon itace

Ta fara sana’ar fim a shekarar 1994 inda ta fara da fim din ta na ‘Glamour Girls’.

Na yi murabus daga ɗirka wa 'yan mata ciki, Mawaƙi 2Baba

A wani labarin, Shaharraen mawakin Najeriya da ya lashe kyaututuka da dama, Innocent Idibia da aka fi sani da 2Baba ya bayyana cewa ba zai sake yi wa wata mace ciki ba, The Nation ta ruwaito.

Mawakin, da ya yi wakar 'African Queen' ya bayyana hakan ne cikin wani bidiyo da ya bazu a kafafen sada zumunta yayin bikin al'adu da kadade ta Idoma International Carnivial da aka yi a Otukpo, garinsu su 2Baba a Jihar Benue.

Asali: Legit.ng

Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel