Mun Baka Awa 48: PDP Za Ta Yi Wa Obasanjo Fallasa Idan Bai Yi Karin Haske Kan Maganan Da Ya Yi Kan Atiku Ba

Mun Baka Awa 48: PDP Za Ta Yi Wa Obasanjo Fallasa Idan Bai Yi Karin Haske Kan Maganan Da Ya Yi Kan Atiku Ba

  • Babban jam'iyyar hamayya a Najeriya, PDP, ta yi martani kan kalaman da aka danganta da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo kan Atiku Abubakar
  • PDP ta bawa Obasanjo awa 48 ya fito ya yi karin bayani game da abin da ya ke nufi idan kuma ba haka ba za ta fada wa duniya ko wanene shi
  • Sanata Walid Jibrin, Shugaban kwamitin amintattu na PDP ne ya yi wannan martanin yana mai Alhaji Atiku Abubakar mutum ne mai mutunci kuma suna fata zai ci zabe a 2023

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ta bukaci tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya yi karin haske kan kalaman da ya furta kan dan takarar shugaban kasarta, Atiku Abubakar ne cewa ya yi kuskure wurin zabensa (Atiku) a matsayin mataimakinsa a 1999, Nigerian Tribune ta rahoto.

Kara karanta wannan

Ba zan bar harkar siyasa ba, mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ga magoya bayansa

A cewar PDPn, idan tsohon shugaban kasar bai yi karin haske kan kalaman da aka danganta da shi ba cikin awa 48, jam'iyyar za ta fada wa yan Najeriya ainihin ko wanene Obasanjo.

Olusegun Obasanjo
Za Mu Fasa Kwai: Mun Bawa Obasanjo Awa 48 Ya Yi Karin Haske Game Da Abin Da Ya Fada Kan Atiku, PDP. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

Da ya ke magana a taron manema labarai a Kaduna a ranar Litinin, Shugaban Kwamitin amintattu na PDP, Sanata Walid Jibrin, kuma ya bayyana cewa an kafa kwamiti don ganawa da gwamnan Rivers Nyesom Wike kan batun mataimakin shugaban kasa.

Ya ce jam'iyyar za ta warware matsalolinta.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cikin sanawar da aka ce tsohon shugaban kasar ne ya fadi game da Atiku da jaridu suka wallafa, shugaban na BoT ya ce shi da PDP na girmama tsohon shugaban kasar.

Amma, cikin gaggawa ya kara da cewa idan za su yi matukar takaici idan har da gaske ne shi ya furta maganganun da aka danganta da shi.

Kara karanta wannan

Babban Kuskuren da na Tafka Shine Zabar Atiku Mataimakina a 1999, Olusegun Obasanjo

Don haka, ya ce, "Ina son kira ga tsohon Shugaba Obasanjo ya fito fili ya maimaita abin da ya ce. Ko an yi kuskuren rahoto abin da ya fada ne ko kuma hakan ya ke nufi.
"Duk da cewa bai karyata abin da aka rahoto ba, za a iya tsammanin rahoton gaskiya ne, amma idan bai fito fili cikin awa 48 ya bayyana menene gaskiya ba, za ka ji sako daga gare mu kuma ba ni da zabi sai dai in fasa kwai in fada wa duniya ko wanene Obasanjo.
"Babu shakka akwai yiwuwar Obasanjo har yanzu yana fushi da Atiku duk da ya taimake shi amma ya datse masa damar yin tazarce na uku, Alhaji Abubakar Atiku dan takarar shugaban kasar mu ne kuma ina tabbatar maka insha Allahu zai zama shugaban kasa a 2023."

2023: Zulum Muke So Ya Zama Mataimakin Tinubu, Masu Ruwa Da Tsaki a APC

Kara karanta wannan

Da dumi-duminsa: Peter Obi ya ziyarci Gwamna Nyesom Wike a Port Harcourt

A wani rahoton, jagoran masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC daga Arewa, Abdullahi Aliyu Katsina ya ce kuri'an jin ra'ayin al'umma da kungiyar ta yi ya nuna cewa zaben gwamnan Borno, Babagana Zulum ne kadai a matsayin mataimakin Ahmed Bola Tinubu zai tabbatarwa APC samun nasara cikin sauki.

Katsina, yayin taron manema labarai da aka yi a jiya a Minna ya ce duk da cewa mutanen Borno ba su son ya tafi saboda ayyukan alheri da ya ke yi a jihar, yi wa kasa hidima zai fi dacewa, Leadership ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164