Sojojin Najeriya sun ce janyewar wasu sojojin Amurka daga ƙasar ba ta nuna cewa haɗin gwiwar tsaro tsakanin Najeriya da Amurka ya lalace ko ya zo karshe ba.
Sojojin Najeriya sun ce janyewar wasu sojojin Amurka daga ƙasar ba ta nuna cewa haɗin gwiwar tsaro tsakanin Najeriya da Amurka ya lalace ko ya zo karshe ba.
Sakataren Sojojin Kasa na Amurka Daniel Driscoll ya gabatar da murabus bayan takun saka da Pete Hegseth, yayin da rahotanni suka ce har yanzu ba a amince da shi ba.
Rikicin da ake yi a Gabas ta Tsakiya na ci gaba da fadada. Amurka da Isra'ila na ci gaba da kai hare-hare kan Iran yayin da take mayar da martani.
Rundunar yan sandan Iran sun cafke wasu mutane da ake zargi da tura bayanan airri ga kasashen Amurka da Isra'ila, an kama mutanen a wurare daban-daban.
A labarin nan, za a ji cewa Isra'ila ta fara murna da sabon harin da ta kai Iran, yayin da ake ci gaba da zuba ruwan bama-bamai a Tel Aviv a yaƙin Gabas ta Tsakiya.
Shugaban Amurka, Donald Trump ya caccaki kasashen Turai da ke kungiyar NATO kan rashin shiga masa fada da Iran. Ya bayyana cewa karshensu ba zai yi kyau ba.
Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron ya yi waya da shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian. Ya bukaci a bude mashigar Hormuz da Iran ta rufe kirif.
Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya wallafa bidiyo ya fadi halin da ya ke ciki ana jita-jitar cewa ya mutu. An gano cewa bidiyon da ya wallafa na gaskiya ne
Kamfanin Saudi Aramco ya nuna rashin tabbas kan fitar da mai a watan Afrilu, yayin da ikon Iran kan mashigar Hormuz ya zama babban tarnaki ga makamashin duniya.
Kasar Iran ta harba makamin Sijjil mai nisan gaske zuwa Isra'ila karon farko tun bayan fara yaki. Makamin na da karfin gaske kuma zai iya shiga Isra'ila a minti 7.
Manyan kamfanonin mai na Amurka sun gargaɗi Donald Trump kan ta'azzarar matsalar makamashi yayin da Amurka da Iran suka ƙi amincewa da tsagaita wuta.
Labaran duniya
Samu kari