Paparoma ya yi Allah-wadai da kisan gillar da ake yiwa Falasdinawa a Gaza

Paparoma ya yi Allah-wadai da kisan gillar da ake yiwa Falasdinawa a Gaza

- Paparoma Francis ya yi Allah-wadai da hare-haren da sojojin Isra'ila suka kaiwa Falasdinawa a Zirin Gaza

- Shugaban darikar katolikan na duniya ya yi wannan jawabi ne bisa kashe wasu Falasdinawa 60 da raunana 2000 da akayi a ranar Litini da ta gabata

- Paparoman ya ce babbu yadda za'a yi sulhu face an dena kai hare-hare

Jagoran mabiya darikar katolika ta duniya, Paparoma Francis yayi kakkausar suka da Allah-wadai game da kisan gillar baya-bayan nan da sojin haramtaciyyar kasar Isra'ila suka yi wa Falasdinawa a Zirin Gaza.

Paparoma ya yi tir da kisan gillar da ake yiwa mutanen Gaza
Paparoma ya yi tir da kisan gillar da ake yiwa mutanen Gaza

Kamar yadda kamfanin dillancin labaran Reuters suka ruwaito, Paparoma Francis ya yi wannan tsokaci ne yayin da ya ke jawabi a fadarsa ta Vatican inda ya yi tir da harin da sojojin Isra'ilan suka kai kuma ya kara da cewa lokaci ya yi da za'a kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Gabas ta tsakiyar.

KU KARANTA: Babbar mota ta murkushe dalibar jami'a har lahira

Bayan nuna damuwarsa game da kisar da akayi wa Falasdinawan, Paparoman ya kara da cewa babbu yadda za'a zauna teburin sulhu da zaman lafiya alhalin kuma ba'a dena yaki ba.

A dai ranar Litinin din wannan makon ne sojojin HKI suka kai wa Falasdinawan hari inda suka kashe a kalla mutane 60 tare da raunana wasu sama da 2000 a Zirin Gaza a yayin da suke gudanar da zanga-zangar ranar Nakba wanda ta ci karo da lokacin da Amurka ke bude ofishin jakadancin ta a birnin Qudus.

A wata cikin yan kwanakinan, kungiyar hadin kan kasashen Afirka AU itama tayi Allah wadai da hare-haren da Israi'la ta kaiwa Falasdinawan inda ta ce ya zama dole a lallubo hanyoyin da za'a warware matsalolin da ke adabar yankin na Gabas ta tsakiya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164