Shugaban Addinin Kirista Papa Roma Francis ya yi wa 'yan kasar Syria addu'a
- Shugaban Addinin Kirista na shiyyar Katolika ya yi wa kasar Syria addu'a
- Ya rokar musu Allah ya kawo musu dauki na tashin hankalin da suke ciki
- Ya bukaci da a gaggauta dakatar da kai hare-haren da ake yi musu
Shugaban addinin kirista na duniya shiyyar katolika, Papa Roma Francis, ya yi wa kasar Syria addu'ar Allah ya ceto su daga tashin hankali da ukubar da suke ciki.
DUBA WANNAN: Matasa 5 masu neman kujerar Buhari a zaben 2019
Shugaban wanda yayi bayani gaban dubunnan mutanen da suka taru a filin San Pietro dake kasar Vatikan, ya yi batun rikice-rikicen dake karuwa a yanzu haka a kasar Syria.
Ya ce, "Watan Fabrairu ya yi dai-dai da rikici mafi tsanani da munanan tashe-tashen hankulan da aka share kusan sama da shekara 7 ana tafkawa a kasar ta Syria. Abinda yanzu haka kasar take fuskanta ya wuce duk wani tunanin mai tunani. Ina kira da babbar murya da a gaggauta zubar da jinin haka. Sannan ina roko da ayi kokari wajen kai marasa lafiya asibiti sannan kuma a aika wa da mabukatan kayan tallafi."
A karshe, Papa Francis ya yiwa kasar Syria addu'ar Allah ya kawo musu dauki tare da ceto su daga tashin hankalin da suke ciki.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng