2040: Addinin Musulunci zai zamto na biyu mafi yawan mabiya a kasar Amurka

2040: Addinin Musulunci zai zamto na biyu mafi yawan mabiya a kasar Amurka

Wani sabon bincike dam asana suka gudanar a kasar Amurka cewar addinin Musulunci na gab da zama addini mafi girma da yawan jama’a mabiya a kasar, inji rahoton jaridar Newsweek.

Kungiyar masana mai suna Pew Research Centre ta bayyana sakamakon binciken da tayi, inda tace zuwa shekarar 2040, Musulmai zasu wuce yahudawa a kasar Amurka, a matsayin addini na biyu sakamakon karuwar haihuwa da auratayya.

KU KARANTA: Hotunan Attahiru Bafarawa tare da ɗansa yayin da suka shiga Ka’aba

Binciken wanda ya samo tushe tun daga kididdigan jama’an kasar Amurka da aka yi na shekarar 2007, 2011 da 2017, ya nuna yawan Musulmai zai ninka daga miliyan 3.45 zuwa miliyan 8.09, daga yanzu zuwa shekarar 20150.

2040: Addinin Musulunci zai zamto na biyu mafi yawan mabiya a kasar Amurka
Musulman Amurka

Majiyar Legit.ng ta ruwaito mafi yawan mabiya addinin Musulunci, wato Musulmai sun fi yawaita a manyan biranen kasar Amurka, da suka hada da birnin Washington da New York, fiye da sauran garuruwan kasar.

Binciken ya daganta yawan Musulmai ga yawan haihuwa, karuwar Musulmai masu shigowa kasar Amurka daga sauran kasashen Musulmai, musamman masu fama da rigingimu, inda binciken ya kara da cewa kashi 75 na musulman Amurka bakin haure ne.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel