Bayan Gargadin Khamenei, Amurka Ta Sake Tsokano Fada da Kasar Musulunci Ta Iran

Bayan Gargadin Khamenei, Amurka Ta Sake Tsokano Fada da Kasar Musulunci Ta Iran

  • Amurka ta kaddamar da hare-hare kan wasu wuraren Iran da ke mashigar ruwan Hormuz, sa’o’i kadan kafin fara zaben tsakiyar wa’adin mulki
  • Jami’an Amurka sun ce hare-haren na kare kadarorinsu ne a yankin, tare da mayar da martani kan harin da dakarun IRGC suka kai wa jirgin saman Amurka
  • Shugaban majalisar dokokin Iran ya yi gargadin cewa jamhuriyar musulunci ba za ta taba mika wuya ga makiyanta ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Amurka - Amurka ta kaddamar da sababbin hare-hare kan wasu wuraren Iran da ke mashigar ruwan Hormuz, sa’o’i kadan kafin kasar ta gudanar da zaben tsakiyar wa’adin mulki.

Jami’an Amurka sun shaida wa wasu kafafen yada labaran kasar cewa hare-haren na kare kai ne, kuma an kai su ne domin kare kadarorin Amurka da ke yankin.

Kara karanta wannan

Donald Trump ya sa sojojin Amurka kai sababbin hare hare Iran

Trump.
Shugaban kasar Amurka, Donald Ttump da wani jirgin ruwa na yaki Hoto: US Navy
Source: Getty Images

Amurka ta kai hare-hare kan Iran

Tashar Al-Jazeera ta ruwaito cewa jami’an sun kara da cewa hare-haren sun kasance martani ne kan harin da rundunar kare juyin juya halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta kai wa wani jirgin saman Amurka.

Kafin wannan mataki, hare-haren da aka tabbatar Amurka ta kai wa Iran na baya-bayan nan sun faru ne a watan Satumban da ya gabatam

Tun da farko, Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa ba za a sake kai hare-hare ba har sai bayan kammala zaben tsakiyar wa’adin mulki.

Gargadin jagoran addinin Iran

A ranar Asabar, Jagoran addini na Iran, Mojtaba Khamenei, ya umarci sojojin kasar da su mayar da martani kan duk wata barazana, ba tare da takaita martanin da wani yanki ko kasa ba.

Khamenei ya kuma bayar da umarnin fadada jerin wuraren da za a iya kai wa hari a Amurka da Isra’ila, kamar yadda CNN ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ciyaman ya sha da ƙyar da miyagun yan daba suka farmaki wurin zaɓen fitar da gwanin APC

A lokacin da aka bayar da wannan umarni, Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio, ya ce Trump bai yanke shawarar ko zai sake harba makamai masu linzami kan Iran ba.

Sai dai Rubio ya bayyana cewa Trump ya fi son a warware rikicin ta hanyar diflomasiyya.

Matsin lamba kan Shugaba Trump

Trump na fuskantar raguwar goyon baya a sakamakon kuri’un jin ra’ayin jama’a, yayin da wasu daga cikin jam’iyyarsa ke matsa masa lamba ya kawo karshen yakin.

Yakin ya fara ne a watan Fabrairun 2026, bayan da Amurka da Isra’ila suka kai hare-haren hadin gwiwa kan Iran.

Trump.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump da jagoran addinin kasar Musulunci ta Iran, Mojtaba Khamenei Hoto: Anadolu
Source: Getty Images

A wani sabon gargadi da ya fitar da sanyin safiyar Talata, Mohammad Ghalibaf, shugaban majalisar dokokin Iran da ke jagorantar tattaunawar kasar da Amurka, ya ce al’ummar Iran ba za su mika wuya ga barazanar makiya ba.

Ghalibaf ya ce:

“Al’ummar Iran ba za su mika wuya ga barazanar makiya ba.”

Iran ta shirya yaki da Amurka

Kun ji cewa Rundunar IRGC ta Iran ta ce tana shirin bayyana wani sabon makami da ta kira “Uban dukkan bama-bamai” yayin da ake kokarin kawo karshen rikicin kasar da Amurka.

Rundunar IRGC ta bayyana hakan ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun takun-saka tsakanin Tehran da Washington.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262