'Trump na Shirin Amfani da Nukiliya a Iran,' Dan Amurka Ya Yi Tone Tone
- Dan jaridar Amurka, Tucker Carlson ya yi zargin cewa gwamnatin Donald Trump na iya amincewa da kai harin nukiliya kan Iran cikin ’yan kwanaki
- Mai sharhin siyasar ya ce Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, na matsa wa Trump lamba domin ya kai harin kan wani wuri a Iran
- A zargin da ya yi, Carlson ya yi gargadin cewa harin na iya jefa duniya cikin yakin nukiliya, tare da illata tattalin arzikin Gabas ta Tsakiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Washington, Amurka – Wani fitaccen mai sharhin siyasa a Amurka, Tucker Carlson, ya yi ikirarin cewa gwamnatin Shugaba Donald Trump na iya amincewa da kai harin nukiliya kan Iran cikin ’yan kwanaki.
Carlson, wanda ke gabatar da shirinsa mai zaman kansa a dandalin sada zumunta na X, ya ce Netanyahu na matsa wa Trump lamba domin ya amince da kai harin kan tsaunin Pickaxe da ke tsakiyar Iran.

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: Ɗan Majalisar Amurka ya sake ɗauko batun zargin kisan Kiristoci a Najeriya

Source: Getty Images
A wani sako da ya wallafa a X, Carlson ya ce wurin yana karkashin wani katon dutsen granite mai kaurin kusan kafa 300, wanda zai iya hana makaman Amurka na yau da kullum isa ga ramukan da ke karkashinsa.
Netanyahu na matsa wa Trump
Carlson ya yi zargin cewa Netanyahu na tuntubar Trump a kullum domin ya shawo kansa ya kai harin kan wurin da ake zargin Iran na gudanar da ayyukan nukiliya.
Ya nakalto wani mutum da ya ce yana da masaniya kan lamarin yana cewa Netanyahu na kiran Trump a kowace rana kan batun.
Mai sharhin ya kuma yi ikirarin cewa Netanyahu na bukatar taimakon sojin Amurka domin samun rinjayen kujeru 61 a majalisar dokokin Isra’ila, wato Knesset, bayan zaben da aka gudanar.
A cewarsa, Netanyahu na matsa wa Ministan Tsaron Amurka, Pete Hegseth, da shugaban rundunar sojin Amurka ta CENTCOM, Admiral Brad Cooper, lamba domin su dawo da hare-haren soji.
Carlson ya yi gargadi kan illar yakin
Carlson ya bayyana damuwarsa kan yiwuwar amfani da makamin nukiliya, yana mai cewa hakan zai iya jawo mummunar illa ga kasashen yankin Tekun Fasha da sauran duniya.
Ya yi zargin cewa rikicin da aka kwashe wata takwas ana yi ya yi illa ga tattalin arzikin kasashen yankin da kasuwannin makamashi na duniya.
Ya kuma ce wasu manyan jiragen dakon mai guda 11 sun lalace a mashigar ruwan Hormuz a watan Oktoba kadai.
Carlson ya yi gargadin cewa fashewar makamin nukiliya a tsaunin Pickaxe na iya gurbata ruwan Tekun Fasha, lamarin da zai iya barazana ga ruwan sha na mutane miliyan 100.

Source: Getty Images
Ya kuma yi hasashen cewa amfani da makamin nukiliya na farko zai iya haifar da yakin duniya na uku, wanda a cewarsa zai kasance gajere amma mai muni.
Trump na nazari kan lamarin
Carlson ya ce Mataimakin Shugaban Amurka, JD Vance, da wakilin musamman na Trump, Steve Witkoff, na kokarin shawo kansa ya bi hanyar diflomasiyya maimakon kai hari.
Rahoton Yenisafak ya nuna cewa ya bayyana cewa ana iya yanke shawara kan lamarin kafin ranar 7 ga watan Nuwamba.
Sai dai a ranar Asabar, Trump ya shaida wa manema labarai a gidansa na Mar-a-Lago cewa Amurka za ta iya kai hari kan sauran wuraren da ta ke ganin barazana ne cikin mintuna 10.
Bayani kan zaben Isra'ila
A wani labarin, mun ruwaito cewa sakamakon wucin gadi na zaben majalisar dokokin Isra’ila ya nuna cewa Firaminista Benjamin Netanyahu na kan gaba.
Sai dai duk da wannan nasara, jam’iyyar Likud ta Netanyahu da kawayenta na bangaren masu tsattsauran ra’ayin siyasa da Yahudawa masu tsananin ba su kai yawan kujerun kafa gwamnati ba.
Bayan kidayar kashi 99 cikin 100 na kuri’un, jam’iyyar Netanyahu da kawayenta na shirin samun kujeru 53 daga cikin 120 na majalisar Knesset.
Asali: Legit.ng

