An Shiga Tashin Hankali da Kofar Wani Jirgin Sama Ta Fado Kasa bayan Tashinsa a Abuja
- An yi nasarar kauce wa hatsarin jirgin sama bayan ƙofar wani jirgin CL60 mallakin kamfanin Triton Aviation ta faɗo jim kaɗan bayan tashinsa daga Abuja
- Ma’aikatan jirgin sun ayyana dokar ta-baci ta “Mayday” yayin da jirgin ke shawagi a tsawon ƙafa 3,000 a sararin samaniya
- Jirgin ya yi nasarar komawa filin jirgin saman Abuja, inda ya sauka lafiya a titin saukar jiragen sama na 22 da misalin ƙarfe 4:34 na yamma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Wani jirgin sama mallakin kamfanin Triton Aviation ya tsallake rijiya da baya bayan tashinsa daga filin saukanda tshin jiragen sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.
An ruwaito cewa jirgin CL60 ya tsira daga yiwuwar hatsari bayan kofarss ta buɗe tare da faɗowa jim kaɗan bayan tashinsa, lamarin da ya tilasta wa ma’aikatan jirgin ayyana dokar ta-baci ta “Mayday”.

Kara karanta wannan
"Sun tsorata," Kwankwaso ya gano sasu shirin maguɗi a zaɓen shugaban ƙasa na 2027

Source: Facebook
Daily Trust ta rahoto cewa jirgin mai lambar rajista T7-SEI, ya shirya tafiya daga Abuja zuwa filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas lokacin da lamarin ya faru da misalin ƙarfe 4:20 na yamma agogon UTC.
Yadda jirgin ya rasa kofarsa
Wani rahoton abin da ya faru ya nuna cewa jirgin ya tashi daga titin tashin jiragen sama na 22 da ƙarfe 4:17 na yamma agogon UTC.
A lokacin da lamarin ya faru, jirgin yana da nisan mil uku na ruwa daga filin jirgin saman, kuma yana hawa zuwa tsawon ƙafa 3,000.
A cewar rahoton, ma’aikatan jirgin sun sanar da masu kula da zirga-zirgar jiragen sama cewa wata ƙofa ta buɗe yayin da jirgin ke tashi zuwa sama.
Hakan ya sa mai kula da zirga-zirgar jiragen sama ya umurci jirgin da ya koma Abuja domin saukar gaggawa, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Matakan da aka dauka kafin saukar jirgin
Bayan kiran neman agajin gaggawa, an sanar da sashen kashe gobara na filin jirgin da ma’aikatan lafiya, tare da umartar su da su kasance cikin shirin ko-ta-kwana.
Haka kuma, an umurci jami’an kashe gobara da na agajin gaggawa da su koma wuraren da aka ware musu na A4 da A5 domin shirin karɓar jirgin idan ya dawo.
“Jirgin ya sauka lafiya a titin saukar jiragen sama na 22 da misalin ƙarfe 4:34 na yamma agogon UTC, mintuna 14 bayan kiran neman agajin gaggawa na Mayday.”
Rahoton ya ƙara da cewa bayan jirgin ya sauka, mai kula da zirga-zirgar jiragen da ke bakin aiki ya lura cewa ƙofar ta ɓace daga jikin jirgin, abin da ya tabbatar da tsananin lamarin.

Source: Getty Images
A wani rahoto makamancin haka, wani bidiyo da ya yaɗu a kafafen sada zumunta ya nuna cewa wasu manoma sun gano ƙofar jirgin da ta fadi a wata gona da ke cikin Abuja.
Jirgin Enugu Air ya samu tangarda
Kun ji cewa fasinjoji 68 sun shiga firgici bayan jirgin Enugu Air ya yi saukar gaggawa a filin jirgin sama na Benin a jihar Edo.
Wata majiya a filin jirgin saman Benin ta shaida cewa jirgin ya wuce karshen titin saukar jirgi bayan sauka, sannan ya shiga wani daji da ke kusa.
Asali: Legit.ng
