Houthi Ta Zafafa Hare Hare kan Saudiyya, Ta Yi Gagarumar Barna
- An kashe mutum ɗaya, wasu takwas sun jikkata a harin da aka kai filin jirgin saman King Fahd da ke Dammam
- A wani hari daban, mutane biyu sun mutu bayan da makamin tsaron sararin samaniyar Saudiyya ya tare wani jirgi marar matuƙi da ke nufar cibiyar mai ta Shaybah
- Amurka ta umarci wasu jami’an diflomasiyyarta da ’yan uwansu su fice daga ofisoshinta da ke Saudiyya saboda barazanar ƙarin hare-hare
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Dammam, Saudiyya - An kashe mutum ɗaya, wasu takwas kuma sun jikkata a wani hari da aka kai filin jirgin saman King Fahd da ke birnin Dammam, a gabashin Saudiyya.
Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Saudiyya (GACA) ce ta sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba, 21 ga watan Oktoban 2026.

Kara karanta wannan
Abin da cutar Ebola ke yi a jikin dan adam, da yadda za ku kare kan ku daga kamuwa

Source: Getty Images
Sanarwar ta ce waɗanda suka jikkata sun samu raunuka daban-daban, daga ƙanana zuwa masu tsanani, kuma an garzaya da su asibitoci domin samun kulawar likitoci, tashar Aljazeera ta kawo rahoton.
Mutane 2 sun mutu a wani hari
Tun da farko a ranar Laraba, mutane biyu sun mutu bayan da rundunar tsaron sararin samaniyar Saudiyya ta tare wani jirgi marar matuƙi da ke ƙoƙarin kai hari kan wata cibiyar da ke filin haƙar mai na Shaybah, mallakin kamfanin mai na Saudi Aramco.
Ma’aikatar Makamashi ta Saudiyya ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar bayan aukuwar lamarin.
Harin na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun ƙarin hare-hare kan filayen jiragen sama na Saudiyya, yayin da rikici tsakanin mayakan Houthi da gwamnatin Yemen da ƙasashen duniya suka amince da ita, wadda Saudiyya ke marawa baya, ke ƙara tsananta.
An taɓa kai hare-hare a Riyadh
A makon da ya gabata, Saudiyya ta sanar da cewa wani harin makami da aka kai filin jirgin saman King Khalid da ke Riyadh a ranar 11 ga Oktoba ya yi sanadin mutuwar mutum ɗaya da jikkata wasu 11.
Haka kuma, a ranar 10 ga Oktoba, hukumar kula da sufurin jiragen saman ƙasar ta bayyana cewa wani harin daban da aka kai filin jirgin saman ya kashe mutane 12 tare da jikkata fiye da 300.
Waɗannan hare-hare na ƙara nuna tsananin matsalar tsaro da Saudiyya ke fuskanta a yayin da rikicin yankin ke ƙamari.
Amurka ta umarci jami’anta su bar Saudiyya
A ranar Laraba, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta umarci jami’an diflomasiyyarta da wasu daga cikin ’yan uwansu da ke ofisoshinta a Saudiyya su fice daga ƙasar, sakamakon hare-haren da mayakan Houthi ke ci gaba da kaiwa.
Jami’an Amurka sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa akwai kuma shirin janye ’yan uwan wasu jami’an da ke aiki a wasu ofisoshin diflomasiyyar Amurka a yankin.
A nata ɓangaren, ofishin jakadancin Amurka da ke Riyadh ya fitar da sanarwar tsaro a ranar Laraba, inda ya yi gargaɗi kan yiwuwar sake kai wasu hare-hare da mayakan Houthi za su iya kaiwa Saudiyya.

Source: Getty Images
Houthi ta kai hari a Saudiyya
A wani labarin kuma, kun ji cewa Houthi ta Yemen ta yi ikirarin cewa ta kai hari kan wata babbar cibiyar man fetur a Saudiyya da makamai masu linzami masu cin dogon zango da jirage marasa matuƙa.
An kai hare-haren ne a matsayin martani ga hare-haren sama da Saudiyya ke kai wa yankunan Yemen da Houthi ke iko da su, ciki har da babban birnin ƙasar, Sanaa.
Asali: Legit.ng

