Ukraine na Ta shiga Uku, Trump Ya Gudu Ya Bar Ta Putin na Mata Ruwan Wuta
- Volodymyr Zelensky ya ce yana jin Shugaban Amurka Donald Trump ya ci amanarsa bayan Amurka ta amince da sassauta takunkumi kan shigo da man dizal daga Rasha
- Zelensky ya sanar da cewa Ukraine za ta sake kai hare-hare kan matatun man Rasha, yana mai cewa an cire takunkumin da aka sanya wa irin wadannan hare-hare
- Shugaban Ukraine ya kuma soki matakin Amurka na dakatar da wasu bayanan leken asiri da takaita wasu ayyukan intanet na tauraron Starlink ga kasar shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Kyiv – Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya bayyana cewa yana jin kamar Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ci amanarsa, tare da gargadin cewa shugaban Amurkan ya zama kamar sawun keke.
Zelensky ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin da takun saka tsakanin kasashen biyu ke kara tsananta, sakamakon matakan da gwamnatin Trump ta dauka kan yakin Ukraine da Rasha.

Source: Getty Images
CNN ta wallafa cewa shugaban Ukraine ya ce yana bakin cikin rasa Amurka a matsayin amintacciyar abokiyar hulda, yana mai cewa matakin Trump na kulla yarjejeniya da Rasha ya haifar da damuwa a Kyiv.
Zelensky: 'Trump ya ci amana'
Da yake zantawa da mai gabatar da shirye-shirye Piers Morgan, an tambayi Zelensky ko yana ganin gwamnatin Trump ta ci amanar Ukraine.
Ya amsa da cewa:
“Eh,”
Zelensky ya ce:
“Abin takaici ne yadda muka rasa abokin hulda mai karfi.”
Ya kuma bayyana cewa lamarin yana masa zafi saboda Ukraine ce kasarsa, gidansa da kuma inda ’ya’yansa suke, yana mai cewa zai jin zafi idan Trump ya zabi bangare guda a rikicin.
“Idan kana tsakiyar rikici, ya kamata ka tsaya a tsakiya, ba a bangaren da ba daidai ba. Wannan ba shi ne bangaren da tarihi zai dauka a matsayin daidai ba,”
In ji Zelensky.
Rasha ta cigaba da kai hare-hare kasar Ukraine duk da maganar tsagaita wuta da Trump ya yi a 'yan kwanakin nan.
Ukraine za ta kai hari Rasha
A wata hira da jaridar Financial Times a Landan, Zelensky ya bayyana cewa Ukraine za ta sake kai hare-hare kan matatun man Rasha.
Ya ce:
“An cire takunkumin da aka sanya kan kai hare-hare kan matatun man. Mun gama da wannan.”
Kalaman na zuwa ne bayan Trump ya amince da sassauta takunkumi kan Rasha domin Amurka ta shigo da man dizal daga kasar, yayin da yake matsa wa Ukraine lamba ta dakatar da hare-haren da take kai wa wuraren sarrafa man Rasha.

Source: Getty Images
Trump ya danganta hauhawar farashin makamashi da hare-haren Ukraine kan matatun man Rasha, maimakon yakin da ake yi da Iran.
A ranar Asabar, Trump ya kuma ce Ukraine na bukatar sabon shugaban kasa, lamarin da ya kara tsananta rashin jituwar da ke tsakanin shugabannin biyu.
Trump ya nuna damuwa kan Iran
A wani labarin, kun ji cewa Shugaban Amurka Donald Trump ya ce mai yiwuwa kasarsa ta wuce gona da iri wajen kai hari kan shugabannin Iran.
Trump ya bayyana hakan ne yayin wani taron yakin neman zabe a jihar Ohio, inda ya ce Amurka na fuskantar wahala wajen gano mutanen da za ta tattauna da su a Iran.
Ya kuma yi ikirarin cewa babu wanda ke son zama shugaban kasar, duk da cewa Masoud Pezeshkian ne shugaban Iran tun watan Yulin 2024.
Asali: Legit.ng


