Shugaban Kasar Ukraine, Volodymyr Zelensky, Ya Yi Hadarin Mota a Kyiv

Shugaban Kasar Ukraine, Volodymyr Zelensky, Ya Yi Hadarin Mota a Kyiv

  • Haɗarin mota ya rutsa da shugaban ƙasar Ukraine, Volodymyr Zelensky, a birnin Kyiv yayin da ayarin motocinsa ke wucewa
  • Kakakin shugaban kasar, Sergiy Nikiforov, yace Likitoci sun tabbatar da cewa bai ji wasu munanan raunuka ba a haɗarin
  • Tuni dai jami'am tsaro suka dukufa bincike don gano musabbabin abinda ya haddasa haɗarin

Wani Direban Motar Haya ya yi taho mu gama da Motar dake ɗauke da shugaban ƙasar Ukraine, Volodymyr Zelensky, yayin da Ayarin Motocinsa ke wucewa a birnin Kyiv.

Channels tv ta ruwaito cewa a wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasan, Sergiy Nikiforov, ya fitar da safiyar Alhamis ɗin nan, yace shugaban bai ji wani rauni mai muni ba a haɗarin.

Shugaban ƙasar Ukraine, Volodymyr Zelensky.
Shugaban Kasar Ukraine, Volodymyr Zelensky, Ya Yi Hadarin Mota a Kyiv Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

"A birnin Kyiv, wata Motar Fasinjoji ta yi karo da Motar shugaban ƙasar Ukraine da masu masa rakiya," Inji kakakin Zelensky.

Kara karanta wannan

Ambaliyar Ruwa Ta Tashi Al'ummar Garuruwa Sama da 10 a Jigawa, Ta Cinye Rayukan Mutane

"Likitocin dake cikin ayarin shugaban ƙasan sun yi gaggauwar kai ɗauki ga direban Motar Fasinja da lamarin ya rutsa da shi daga bisani kuma suka ɗora shi a Motar Asibiti."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Likita ya duba shugaba Zelensky, babu wani mummunan rauni da aka samu a jikinsa. A halin yanzun jami'an tsaro sun duƙufa binciken musabbabin da ya haddasa haɗarin."

Sojojin sun ba da mamaki - Zelensky

A wani bidiyo da aka saki bayan haɗarin, shugaban ƙasan ya yi wani jawabi a gidan Talabijin yana mai cewa bai jima da dawowa daga yankin Kharkiv ba, kamar tadda Dailytrust ta ruwaito.

Ya ƙara da cewa, "Kusan baki ɗaya kewayen yankin ya dawo hannu," bayan ruwan wutan da ya tilasta wa Sojojin Rasha barin yankin.

"Wannan babban Motsi ne daga Sojojin mu, Ukraniyawa sun sake ba da mamaki wajen yin abinda ake tsammanin ba zai yuwu ba," inji Zelensky.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Tsagin Wike Sun Bazo Wuta, Atiku Ya Kafa Sharuɗdan Tunɓuke Shugaban PDP Na Ƙasa

A wani labarin kuma kun ji cewa 'Yan Sanda Sun Kama Wani Kwararren Likita Dake Kashe Majinyata Don Sace Motocinsu

Jami'an hukumar yan sanda reshen jihar Edo sun kama wani kwararren Likita dake kashe Direbobi don ya sace Motocinsu.

Kakakin hukumar yan sanda, SP Nwabuzor, yace Likitan mai suna, Abbas Adeyemi, ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel