Amurka za Ta Harbe Tsohon Sojanta a Irin Yanayin da ba a Taba Gani ba a Duniya
- Sakataren Tsaron Amurka, Pete Hegseth, ya bayyana cewa za a nuna kisan wani tsohon kwararre a aikin sojan ƙasar da bindiga kai tsaye ga ma'aikata da jama'a
- Nidal Hasan, wanda ya kashe sojoji 13 a sansanin sojoji na Fort Hood a shekarar 2009, shi ne mutumin da za a gudanar da hukuncin a kansa
- Wannan mataki na nuna hukuncin kisa a fili ta kafar sadarwa ana ganin shi ne irinsa na farko a Amurka a kusan tsawon shekaru 100
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Washington – Ma'aikatar Tsaron Amurka ta sanar da cewa al'umma za su samu damar kallon yadda za a aiwatar da hukuncin kisa ta hanyar harbin bindiga kan wani tsohon soja.
Ministan Tsaron Amurka, Pete Hegseth, ya tabbatar da cewa za a gudanar da wannan kisa ne a kan Nidal Hasan, wanda ya kashe sojoji 13 a sansanin Fort Hood a shekarar 2009.

Kara karanta wannan
Kasurgumin dan bindiga da yaransa 6 sun hadu da abin da ya fi ƙarfinsu, sun mutu nan take

Source: Getty Images
BBC ta rahoto cewa wannan mataki na nuna kisa gaba da gaba a kafar sadarwa ya kasance "abin da ba a taba ganin irinsa ba a wannan zamani," kuma yana fuskantar matsin lamba na fannonin shari'a daga lauyoyi.
Za a saki bidiyon harbe Hasan
Minista Hegseth ya bayyana a lokacin wata hira cewa dakarun soji ne da kansu za su aiwatar da harbin idan ranar ta zo.
Ya bayyana cewa:
"Za mu tabbatar da cewa mutane sun samu damar kallo a fili. Yanayin da mutane za su fahimci cewa akwai sakamako mai tsani ga irin wadannan abubuwa."
Trump ya yarda da hukuncin
Matakin dai ya samu amincewar Shugaban Ƙasa Donald Trump bayan shawarwarin da ministan tsaron ya gabatar gabanin aiwatar da kisan da aka tsara a ranar 3 ga watan Disamba a sansanin Fort Hood da ke Texas.
Hasan, wanda tsohon likitan kwakwalwa ne a rundunar sojin Amurka, ya amsa laifinsa na buɗe wa abokan aikinsa wuta a ginin duba lafiyar sojoji.

Kara karanta wannan
Dubu ta cika: An kama wanda ya kashe malamin addinin Musulunci a Arewacin Najeriya

Source: Getty Images
Duk da haka, ABC ta wallafa cewa masana shari'a irinsu John Mills sun nuna cewa tsarin daukaka shari'a na Hasan bai kammala ba tukuna a kotunan tarayya, lamarin da ka iya tsaida aiwatar da kisan.
Amurka ta rasa jirage 81
A wani labarin, mun ruwaito cewa aƙalla jiragen yaƙi da na leƙen asiri guda 81 na sojojin Amurka ne aka lalata ko aka harbo a lokacin gudanar da samamen 'Operation Epic Fury' da ƙasar ta ƙaddamar kan Iran.
Rahoton da ofishin kasafin kudin majalisar dokokin Amurka (CBO) ya fitar ya nuna cewa asarar da aka yi wa rundunar sojin saman Amurka a yaƙin tsakaninta da Isra'ila a kan Iran ta kai tsakanin dala biliyan 1.9 zuwa dala biliyan 3.3.
Masana harkar tsaro sun bayyana cewa wannan adadi na nuna irin gagarumar asara da ma'aikatar tsaro ke ci gaba da fuskanta yayin da aka kasa samun daidaito kan tsagaita wuta har zuwa yanzu.
Asali: Legit.ng