Gwamnati zata siya jirgin yaki daga kasar Pakistan

Gwamnati zata siya jirgin yaki daga kasar Pakistan

A daidai lokacin da gwamnati ke kokarin magance ta’addanci da matsalar tsageru a kasar nan, da alama shugaban kasa na yunkurin kara habbaka kokarin gwamnatinsa don ganin ana samar ma hukumomin tsaron kasar ingantattun kayan aiki.

Gwamnati zata siya jirgin yaki daga kasar Pakistan

Jaridar Internation Business Times ta ruwito cewa Najeriya na shirin siyan jirgin yaki kirar JF-17 mai aman wuta daga kasar Pakistan. Tun dama kasar Najeriya ta sanya hannu kan yarjejeniya da kasar Amurka don siyan jirgin.

Kamar yadda wata hukumar harkokin kudi ta HIS ta bayyana cewa za’a karkare cinikin siyan jirgin a watan Nuwamba. A daidai wannan lokacin za ayi wani taron bajakolin makamai a Karachi. Da hadin gwiwar kamfanin jirgi na kasar China da na Pakistan aka suka kera jirgin. Idan ba’a manta ba, gwamnatin kasar Amurka  karkashin shugaba Barack Obama taki siyar ma kasar Pakistan jirgin yaki kirar F-16.

KU KARANTA: Rundunar sojan sama ta hallaka yan Boko Haram 300

Wani babban jami’in ma’aikatan tsaro na Pakistan da yayi magana kan batun cinikin, ya ki bayyana iya adadin yawan jiragen da Najeriya zata siya.

Sai dai, tun a watan janairu ne gwamnatin tarayya ta nuna a cikin kasafin kudinta cewa zata siya jiragen yaki kirar JF-17 da kirar Mushshak guda 10, sa’annan kasar China da Pakistan ne ke kera jiragen, a yanzu haka ma China ta fara kera JF-17 din a kamfanin jiragen sama na Pakistan.

Amma jirgin na amfani ne da wani injin kasar Rasha ma suna Klimov RD-93. Jirgin kuma na dauke da makami mai linzami kirar kasar China mai suna PL-12/SD-10 wanda keda dogo da gajeren zango. Bugu da kari za’a iya daukan jirgin da na’urar AIM-9P kamar yadda rahoton ya bayyana.

A kwanakin baya hukumar tsaro ta kasar Pakistan tayi bajakolin jirgin a sararin samaniyar nahiyar Afirka, a sansanin rundunar sojan sama dake garin Waterkloof , Afirka ta kudu. A wani sanarwa da kasar China ta fitar ta bayyana irin abubuwan da jirgin zai iya yi,wanda hakan ne ya sanya su kera shi. Zuwa yanzu dai ba’a tabbatar da yawan kasashen Afirka dake neman siyan jirgin ba.

Gwamnati zata siya jirgin yaki daga kasar Pakistan

Wani rahoton jaridar Premium Times ya bayyana cewa daya daga cikin manufofin taro akan kasafin kudi da gwamnatin ta hada, shi ne hanyoyin samun kudaden shiga ta yadda za’a kashe kudaden da suka kai dala biliyan 10 zuwa 15 don habbaka tattalin arzikin kasa.

Ministan kasafin kudi da tsare tsare, Udoma Udoma yace hanyoyin samun kudin basu wuce a siyar da wasu daga cikin kadarorin gwamnati ba, ko kuma jinginar da wasu kadororin gwamnati, tare da kashe kudaden da aka kwato daga barayin gwamnati.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng