An Nada Sabon Shugaban Sojoji a Kasar Nijar bayan Shirin Kifar da Janar Tiani

An Nada Sabon Shugaban Sojoji a Kasar Nijar bayan Shirin Kifar da Janar Tiani

  • Shugaban mulkin sojin Nijar, Janar Abdourahamane Tiani, ya naɗa sabon shugaban hafsan sojin ƙasar bayan dakile wani yunkurin tawaye da ya girgiza mulkinsa a watan da ya gabata
  • Gwamnatin sojin ta samu nasarar dakile tawayen ne da taimakon ’yan haya na Rasha, bayan an gwabza kazamin yaƙi a wasu sassan babban birnin ƙasar, Yamai
  • Sabon shugaban hafsan sojin, Birgediya Janar Mamane Sani Kiaou, ya taɓa riƙe wannan matsayi, inda yanzu zai maye gurbin Janar Moussa Salaou Barmou.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Niger – Shugaban mulkin sojin Nijar, Janar Abdourahamane Tiani, ya naɗa sabon shugaban hafsan sojin ƙasar bayan dakile wani yunkurin tawaye da ya faru a babban birnin Yamai a watan da ya gabata.

Kara karanta wannan

Houthi sun kwace yankin Bab al Mandab yayin da Saudi ke naman agajin Trump

Gwamnatin sojin ta dakile yunkurin tawayen ne da taimakon ’yan haya na Rasha, bayan wasu sojoji da ba su gamsu da tsarin mulkin ba sun kai hari kan muhimman wurare a Yamai.

Shugaban kasar Nijar
Abdourahamane Tiani a Nijar. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

An naɗa hafsan soji a Nijar

Vanguard ta ruwaito cewa gidan talabijin na ƙasar ya sanar da naɗin Birgediya Janar Mamane Sani Kiaou a matsayin sabon shugaban hafsan sojin Nijar.

Sanarwar ta ce an naɗa Kiaou ne bisa wata doka da Janar Tiani ya sanya wa hannu ranar 11 ga Satumba 2026.

Kiaou zai maye gurbin Janar Moussa Salaou Barmou, wanda sanarwar ba ta bayyana dalilin cire shi daga mukamin ba.

Wani sauyin da Tiani ya yi

Sanarwar ta ƙara da cewa Janar Abdourahmane Abou Zataka zai maye gurbin Kiaou a matsayin shugaban hafsan sojojin ƙasar.

Kiaou ya taɓa jagorantar sojojin Nijar, kuma an bayyana shi a matsayin ƙwararren kwamandan yaƙi da ya samu gogewa wajen tunkarar ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi.

Punch ta wallafa cewa ya jagoranci yaƙi da ƙungiyoyin jihadi a yankin Tillaberi da ke yammacin Nijar da kuma yankin Diffa da ke kudu maso gabashin ƙasar.

Kara karanta wannan

"A wasu lokutan," Ana zargin ba Shugaba Tinubu ke tafiyar da mulkin Najeriya ba

Ayyukan da Kiaou ya yi a baya

Kafofin yaɗa labarai na Nijar sun ruwaito cewa Kiaou ya kammala rangadin wasu muhimman sansanonin sojin ƙasar a baya-bayan nan.

Wasu rahotanni sun bayyana cewa manufar rangadin ita ce “dawo da haɗin kai tsakanin sojoji” bayan rikicin da ya faru a ƙasar.

Shugabannin kasashen Sahel
Shugabannin kasashen Mali, Nijar da Burkina Faso. Hoto: Getty Images
Source: Twitter

An bayyana cewa Kiaou ya kuma jagoranci tattaunawar da ta kai ga janye sojojin Faransa da Amurka daga Nijar bayan juyin mulkin watan Yuli 2023.

An yi harbe harbe a Nijar

A wani labarin, kun ji cewa ma’aikatar Tsaron Nijar ta sanar da cewa wasu sojoji sun yi harbe-harbe a wasu muhimman wurare a Yamai a wani abu da ake zargin yunkurin tawaye ne.

An ji karar harbe-harbe da fashe-fashe a sassa daban-daban na babban birnin da sanyi safiya, lamarin da ya jawo martani daga gwamnatin kasar.

Maharan sun kai hari filin jirgin saman Diori Hamani da ke kuma ɗauke da sansanin soji, tare da yunƙurin kutsawa fadar shugaban ƙasa kafin jami’an tsaron fadar su fatattake su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng