Gwamnatin Najeriya Ta Tsoma Baki kan Harin Houthi a Saudiyya, Ta ba da Shawara

Gwamnatin Najeriya Ta Tsoma Baki kan Harin Houthi a Saudiyya, Ta ba da Shawara

  • Gwamnatin Najeriya ta yi Allah-wadai da sabon harin Houthis kan Saudi Arabia, wanda ya jikkata mutane 73 tare da lalata wata cibiyar mai
  • Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya ta ce sabon rikicin barazana ne ga zaman lafiyar yankin da samar da makamashi a duniya.
  • Najeriya ta bukaci bangarorin da ke rikici su mutunta dokokin kasa da kasa, su kame kansu, sannan su guji matakan da za su cutar fararen hula

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Gwamnatin Najeriya ta yi magana game harin kungiyar Houthis a kasar Saudiyya da ke yankin Gabas ta Tsakiya.

Najeriya ta yi Allah-wadai da sabon harin da kungiyar ‘yan tawayen Yemen ta kai kan Saudi Arabia, wanda ya jikkata mutane 73 tare da lalata cibiyar mai.

Gwamnatin Najeriya ta yi magana kan harin Houthi a Saudiyya
Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Najeriya ta soma baki kan harin Houthi

Kara karanta wannan

‘Dan takarar shugaban kasa a PRP ya ce gara mulkin soja da tsarin yau

Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ta fitar a daren Talata, inda ta gargadi al’ummar duniya kan illar rikicin.

Ma’aikatar ta ce karuwar rikicin na iya yin illa ga zaman lafiyar yankin da kuma samar da makamashi a duniya, tare da barazana ga ikon Saudi Arabia.

Najeriya ta bayyana sabbin tashe-tashen hankulan a matsayin “serious threat”, wato babbar barazana, sannan ta bukaci bangarorin da ke fada su mutunta dokokin kasa da kasa.

Ta kuma bukaci bangarorin su nuna matukar kamewa tare da kauce wa duk wani mataki da zai kara ruruta rikicin ko jefa rayukan fararen hula cikin hadari.

Kungiyar Houthis ta kai hare-hare kan birane biyar a Riyadh, yayin da kuma take kai hare-hare kan jiragen dakon mai a yankin Red Sea.

A lokacin da ta tabbatar da harin ranar Litinin, kungiyar ta ce ta kai hari kan kamfanin mai na kasar Saudi Arabia a Abha da Najran, kusa da iyakar Yemen.

Kungiyar ta kuma ce ta kai hari kan cibiyar kamfanin Aramco da ke Jizan, tare da amfani da jirage marasa matuka da makamai masu linzami wajen kai farmaki.

Kara karanta wannan

Yan daba sun farmaki ofishin jam'iyyar NDC, sun lalata kayan miliyoyi

A cewar Al Jazeera, Houthis ta ce ta gudanar da wani gagarumin farmaki cikin yankunan Saudi Arabia, inda ta kai hari kan sansanin soji.

An kai harin ne kan sansanin sojin sama da ke birnin Khamis Mushait, wanda ke kudancin Saudi Arabia, a cewar rahotannin da aka fitar.

Yawan fararen hula da harin ya shafa na nuna cewa wannan na daga cikin manyan hare-haren da aka kai wa Saudi Arabia cikin shekarun nan.

Hakan ya faru ne musamman bayan da Amurka da Isra’ila suka kaddamar da hare-hare kan Iran a ranar 28 ga Fabrairu, lamarin da ya haifar da ramuwar gayya.

Rahotanni sun ce hare-haren ramuwar gayya sun shafi wuraren da Amurka ke amfani da su a Saudi Arabia da sauran kasashen yankin Gulf.

Saudiyya ta kai hari kan kungiyar Houthi

A wani labarin, an ji cewa kungiyar Houthi ta tabbatar da cewa jiragen yakin Saudiya sun kai hare-haren sama a lardunan Marib, al-Jawf da Taiz na kasar Yemen.

Rahotanni sun ce hare-haren sun biyo bayan wani samame da yan Houthi suka kai kan wuraren makamashin Saudi Aramco.

Rikicin ya zama mafi girma tun bayan yarjejeniyar tsagaita wuta da Majalisar Dinkin Duniya ta shiga tsakani a 2022.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.