Saudi da Kasashen Musulmi 2 Sun Gayyaci Iran Hadaka kan Tsaro
- An ruwaito cewa Iran ta samu gayyata domin shiga sabuwar yarjejeniyar tsaro ta Makkah da Saudiyya, Turkiyya da Pakistan suka kafa a watan Agusta
- Wani babban jami'in Iran ya ce gwamnati na nazarin gayyatar, yayin da har yanzu kasashen da ke cikin yarjejeniyar ba su tabbatar da batun a hukumance ba
- Ana sa ran yarjejeniyar za ta iya fadada zuwa wasu kasashen yankin, yayin da shigar Iran zai iya sauya tsarin wannan sabon kawancen tsaro
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Iran – An ruwaito cewa kasashen Saudiyya, Turkiyya da Pakistan sun gayyaci Iran domin shiga sabuwar yarjejeniyar tsaro ta Makkah, wadda aka kafa a farkon wannan watan.
Rahoton ya ce wani babban jami'in Iran ya tabbatar da cewa kasar ta samu gayyatar, sai dai gwamnatin Iran da kuma kasashen uku da suka kafa yarjejeniyar ba su fitar da wata sanarwa ta hukuma da ta tabbatar da hakan ba.

Source: Getty Images
Jaridar Al Mayadeen ta rahoto cewa shugaban kamfanin dillancin labaran majalisar dokokin Iran, Mehdi Rahimi, ya ce gwamnatin kasarsa tana nazarin batun gayyatar.
Iran ta magantu kan gayyatar
Mehdi Rahimi ya bayyana cewa Iran ta samu gayyata domin shiga yarjejeniyar tsaron, kuma hukumomin kasar suna duba yadda za su tunkari batun.
Ya ce kasashen yankin Gabas ta Tsakiya suna kara fahimtar bukatar samar da wani tsarin tsaro da zai hada kasashen yankin.
Rahimi ya ce wannan ci gaba na da muhimmanci ga Iran, yana mai cewa Tehran ta dade tana kira da a samar da tsarin tsaro na yankin wanda kasashen yankin za su jagoranta.
Jerussalem Post ta wallafa cewa ya ce:
"Iran ta samu gayyata domin shiga Yarjejeniyar Makkah, kuma ana nazarin batun."
Wasu za su iya shiga kawancen
Kasar Turkiyya ta bayyana cewa akwai yiwuwar a fadada yarjejeniyar domin karbar wasu kasashen yankin nan gaba.
An ambaci Masar a matsayin daya daga cikin kasashen da za su iya shiga wannan sabon kawancen tsaro idan har aka fadada shi.

Source: Getty Images
Iran ma ta nuna cewa ba ta da wata babbar damuwa game da kafa yarjejeniyar, inda mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar, Esmaeil Baghaei, ya ce a baya cewa Tehran ba ta da dalilin nuna damuwa kan wannan mataki.
Idan aka tabbatar da gayyatar Iran a hukumance, shigarta cikin kawancen na iya sauya yanayin yarjejeniyar tare da fadada ta zuwa wani babban tsarin tsaron yankin.
Rikicin Kanada da Amurka
A wani labarin kuma, mun ruwaito cewa Firaministan Kanada, Mark Carney, ya yi alkawarin daukar matakin ramuwar gayya bayan Amurka ta kakaba sabon harajin kashi 50 cikin 100 kan wasu kayayyakin kasar.
Carney ya ce Kanada za ta kakaba haraji kan kayayyakin Amurka daidai gwargwado, wanda zai shafi karafa, kayan kiwo, kayan aikin noma, takardu da wasu kayayyakin lantarki.
Ya bayyana cewa gwamnatin Kanada ta yi kokarin cimma yarjejeniya da Amurka domin kare ma'aikata da tattalin arzikinta, amma tattaunawar kasuwanci tsakanin kasashen biyu ta ci tura.
Asali: Legit.ng

