Uganda: Matashi ɗan shekara 19 ya fito takarar shugaban kasa

Uganda: Matashi ɗan shekara 19 ya fito takarar shugaban kasa

Hillary Humphrey Kaweesa dama tun tasowarsa matashi ne mai son jogaranci kuma a halin yanzu ya cika ka'idan jagorancin kasar sa.

Matashin mai shekara 19 ya siya fom din nuna sha'awar shiga takarar zaben shugaban kasa da za a gudanar a kasar Uganda kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Hillary Humphrey Kaweesa ya ce dama ya dade yana jagoranci kuma ya yi imanin zai iya shugabancin kasar.

Matashi dan shekara 19 ya fito takarar shugaban kasa a Uganda
Matashi dan shekara 19 ya fito takarar shugaban kasa a Uganda
Asali: Twitter

Ya ce zai nemi tallafi domin tara kudi har shillings miliyan 20 (Ksh590,900) kudin tikitin shiga takarar zaben.

DUBA WANNAN: Adama Indimi da mijinta sun ziyarci surukinta a fadarsa da ke Kogi (Hotuna)

Ana kuma bukatar Mr Kaweesa ya samu amincewar mutum dari daga ko wanne gunduma inda za su saka masa hannu na amincewa da fitowa takararsa.

Kasar ta Uganda tana da gundumomi guda 100.

Kudin tsarin mulkin kasar Uganda ta bawa ko wane dan kasa mai shekaru 18 da sama damar neman kujerar shugabancin kasar.

Matashin ya shiga sahun su dan majalisa Robert Kyagulanyi da aka fi sani da Bobi Wine da tsohon Janar din Soja Henry Tumukunde wadanda suka nuna shaawar shiga takarar don fafatawa da Shugaba Yoweri Museveni.

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, Tsohon shugaban Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo ya bukaci matasan Afirka su kawar da tsofaffi daga madafan iko a kasashen su.

Obasanjo ya shawarci matasan sun riƙa shiga siyasa a dama da su da nufin karbe mulki daga mazajen na jiya kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Obasanjo ya yi wannan jawabin ne a ranar Laraba yayin da ya ke gabatar da wata lakca yayin bikin ranar matasa da ya aka yi ta yanar gizo.

Cibiyar cigaban matasa, wata bangare na ɗakin karatun shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo da ke Oke-Mosan Abeoluta ne ta shirya taron.

Wadanda suka hallarci taron su fito daga ƙasashen Najeriya, Ghana, Amurka, Mali, Kenya da Afirka ta Kudu.

A cewarsa, muddin ba a tilasta wa tsofaffi barin mulki ba, za su cigaba da rike mulkin ne ba tare da taɓuka wa matasa wani abin azo a gani ba.

Obasanjo ya ce, "Idan ba matse su ku kayi suka sauka daga mulki ba, ba za su sauka ba har da wadanda na shekarun su ya dara 80 za su so su cigaba da zama a kan mulki.

"Irin canjin da nake magana a nan da na ke ganin za mu iya yi shine mu saka a kuɗin tsarin mulkin jam'iyyu cewa dole wani kaso na mukamai matasa ne za su riƙe. Misali ana iya cewa kashi 50 na muƙamai a jam'iyyar masu shekaru ƙasa da 40 ne za su riƙe.

"Ana ma iya inganta abin a ce dukkan waɗanda za a tsayar takara a ƙalla kashi 50 cikin ɗari su kasance wadanda shekarunsu bai haura 40 ba. Wannan fifiko ne mai kyau ga matasa."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel