Amurka Ta Tura Wakili Rasha kan Tsoron Manyan Hare Haren da Putin zai kai

Amurka Ta Tura Wakili Rasha kan Tsoron Manyan Hare Haren da Putin zai kai

  • Daraktan hukumar CIA ta Amurka, John Ratcliffe, ya kai wata ziyarar sirri zuwa Moscow inda aka ce ya gargadi Rasha kan kai hari ga kasashen NATO
  • Bayanan leken asirin Amurka sun nuna yiwuwar Rasha ta kai wani karamin hari a gabashin kasashen NATO, musamman yankin Baltic
  • A ziyarar da ya kai Moscow, Ratcliffe ya kuma tattauna batun Iran tare da jami'an Rasha, yayin da Amurka ke neman rage goyon bayan da Moscow ga Tehran

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Washington, Amurka - Daraktan Hukumar Leken Asiri ta Amurka, CIA, John Ratcliffe, ya kai wata ziyarar sirri zuwa birnin Moscow inda ya gargadi Rasha kan duk wani yunkurin kai hari ga kasashen kungiyar tsaro ta NATO.

Rahotanni sun nuna cewa Ratcliffe ya kai ziyarar ce a farkon wannan mako, yayin da Amurka ke nuna damuwa kan yiwuwar Rasha ta kara fadada rikicin da take yi da Ukraine zuwa wasu kasashen Turai.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Ɗan takarar shugaban ƙasa ya shirya dawo da litar fetur N200 a Najeriya

Vladimir Putin da Donald Trump
Lokacin da Vladimir Putin ya gana da Donald Trump. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

ABC News ta rahoto cewa babban manufar ziyarar ita ce isar da gargadi ga Rasha kan kai hari ga wata kasa da ke karkashin kawancen NATO.

Dalilin zuwan CIA Rasha

Wasu bayanan leken asirin Amurka sun nuna cewa Rasha na iya kai hari a gabashin NATO cikin makonni masu zuwa domin gwada matsayin kawancen wajen mayar da martani.

Rahoton ya ce jami'an Amurka na fargabar shugaban Rasha, Vladimir Putin, zai iya kokarin kara rikici ta hanyar kai wani karamin farmaki ta kasa, musamman a daya daga cikin kasashen yankin Baltic.

Haka kuma akwai fargabar cewa Rasha na iya kai hare-haren intanet kan wasu kasashen gabashin Turai, yayin da yakin Ukraine ya kasa kai ga wata babbar nasara ga bangarorin da ke fafatawa.

Wall Street Journal ta rahoto cewa Ratcliffe ya shafe kusan sa'o'i takwas a Moscow ranar Talata, inda ya tattauna da jami'an leken asirin Rasha.

Shin Ratcliffe ya gana da Putin?

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Matakin da ƙasar musulunci ta Iran ta ɗauka zai shaafi 'yan Najeriya

Fadar Kremlin ta tabbatar a ranar Laraba cewa shugaban CIA ya gana da jami'an leken asirin Rasha, sai dai ta ce bai gana da shugaban kasar, Vladimir Putin ba.

Rahotanni sun ce baya ga batun NATO, Ratcliffe ya kuma tattauna kan Iran tare da jami'an Rasha, inda Amurka ke neman Moscow ta rage goyon bayan soja da tattalin arziki da take bai wa Tehran.

Fadar White House ta ki yin bayani dalla-dalla kan ziyarar, yayin da shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana tafiyar Ratcliffe a matsayin wata ziyara da ba ta da ban mamaki sosai.

A baya dai, tsohon shugaban CIA, William Burns, ya kai ziyara Moscow a watan Nuwamban 2021 domin gargadin Rasha kan mamaye Ukraine, amma daga baya Rasha ta kaddamar da cikakken hari kan Ukraine.

John Ratcliffe tare da Donald Trump
Donald Trump na magana da John Ratcliffe. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

An so yi wa Amurka kutse

A wani labarin, mun ruwaito cewa Ma'aikatar Shari'a ta Amurka da hukumar FBI sun sanar da kwace wasu shafukan intanet da masu kutse ke amfani da su wajen kai hare-hare kan muhimman cibiyoyin kasar.

Hukumomin sun ce an rufe hanyoyin amfani da wasu manhajoji biyu masu suna QScan da QTRouter, wadanda aka ce masu kutse masu alaka da wata kungiyar da China ke daukar nauyi suka kirkira.

Rahoton ya nuna cewa daga cikin cibiyoyin da ayyukan masu kutse suka shafa akwai NASA, babban bankin Amurka, Ma'aikatar Makamashi, Ma'aikatar Shari'a da Majalisar Dattawan Amurka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng