Subhallah: Gwamnatin China ta rusa Masallatai sama da dubu 15 a birnin Xinjiang

Subhallah: Gwamnatin China ta rusa Masallatai sama da dubu 15 a birnin Xinjiang

- Wani bincike da aka gudanar ya nuna cewa gwamnatin kasar China ta ruguza dubban masallatai a yankin Xinjiang

- Cibiyar bincike kan al’amuran yau da kullum mai zaman kanta da ke kasar Australia (ASPI) ce ta bayyana hakan

- An tattaro cewa hukumomin kasar na China sun rusa kimanin Masallatai 16,000 a yankin cikin shekaru uku

Cibiyar bincike kan al’amuran yau da kullum mai zaman kanta da ke kasar Australia (ASPI), ta ce gwamnatin China ta ruguza dubban masallatai a yankin Xinjiang.

Cibiyar ta wallafa rahoton ne a ranar Juma'a, 25 ga watan Satumba.

KU KARANTA KUMA: Takarar shugaban ƙasa 2023: Manzo Ayodele ya faɗi abunda zai faru da Tinubu

Subhallah: Gwamnatin China ta rusa Masallatai sama da dubu 15 a birnin Xinjiang
Subhallah: Gwamnatin China ta rusa Masallatai sama da dubu 15 a birnin Xinjiang Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta sha wallafa bayanai kan irin cin kashin da kasar ke yi wa Musulmi da sauran kabilu marasa yawa a yankin na Xinjiang.

Cibiyar tace ta tattara bayananta ne ta wajen amfani da hotuna daga tauraron dan adam wadanda suka nuna cewar hukumomin kasar sun rusa Masallatai kusan 16,000 a yankin.

Hakan ya wakana ne a cikin shekaru uku da suka shige, sashin Hausa na RFI ta ruwaito.

Rahoton ya kara da cewar ko guda ba a taba wani wajen ibada na mabiya addinin Buddah ko kuma Mujami’u ba.

KU KARANTA KUMA: Manyan abubuwa 4 da suka faru bayan rasuwar Sarkin Zazzau Shehu Idris

Zuwa yanzu sun rusa kaso daya bisa uku na wuraren ibadan Musulmai, musamman ma a biranen Urumqi da Kashgar da ke Xinjiang.

Kungiyoyin kare hakkin bil'adama sun dade suna zargin kasar China da garkame Musulmai ‘yan kabilun Uighur da Turkic su sama da miliyan daya.

An tsare su ne a wasu sansanonin da ke arewa maso yammacin kasar da aniyar tursasa musu barin addini da al’adunsu.

A wani labarin, mun kawo maku cewa mazauna babban birnin Fuyu na China sun sha matukar mamaki da al'ajabin abinda ya faru a kasar.

Kamar yadda aka saba dai, rana daya ce ke fitowa sannan ta fadi, amma ba hakan bane ya faru a makon. Rana uku ne suka bayyana kuma suka dinga haskawa, abun cike da mamaki.

Wasu manyan kwallayen haske suka bayyana a kowanne gefe na rana, hakan kuwa ya disashe hasken ranar don sune suka dinga haskawa.

Wannan lamarin ya faru ne a ranar karshe ta shekarar 2019 a yankin Jilin dake Arewa maso gabas na kasar.

Kamar yadda CGTN suka bayyana, rana uku sun bayyana a sararin samaniya a arewa maso gabas na China.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel