Mataimakin Shugaban Kasa a Afrika Ya Yi Murabus Watanni bayan Hawa Mulki
- Mataimakin shugaban kasar Tanzania, Emmanuel Nchimbi, ya sanar da yin murabus daga mukaminsa, kasa da watanni 10 bayan rantsar da shi
- Nchimbi ya ce ya yanke shawarar yin murabus ne domin mutunta bukatar Shugaba Samia Suluhu Hassan na samun sauyi a ofishin mataimakin shugaban ƙasa
- Murabus ɗin ya sa Nchimbi ya zama mataimakin shugaban ƙasa na farko a tarihin Tanzania da ya sauka daga mukamin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Kasar Tanzania - Mataimakin Shugaban Tanzania, Emmanuel Nchimbi, ya sanar da yin murabus daga mukaminsa.
Murabus dinsa na zuwa ne makonni bayan rahotannin da suka bayyana cewa dangantakarsa da Shugaba Samia Suluhu Hassan ta fara samun matsala.

Source: Instagram
Nchimbi mai shekaru 54 ya wallafa gajeriyar wasiƙar murabus ɗinsa a shafinsa na Instagram ranar Talata, 25 ga watan Agustan 2026 inda ya ce ya yanke shawarar sauka daga mukamin ne domin mutunta buƙatar shugaban ƙasar.
Majiyoyi daga ofishinsa da kuma Fadar Shugaban Ƙasa sun tabbatar da matakin.
Zai bar harkokin gwamnati
Emmanuel Nchimbi ya ce zai yi ritaya daga harkokin gwamnati a ƙarshen mako mai zuwa.
Murabus ɗin nasa ya zo ne kasa da watanni 10 bayan rantsar da shi a matsayin mataimakin shugaban ƙasa, lamarin da ya sa ya zama mutum na farko da ya taɓa yin murabus daga wannan mukami a tarihin Tanzania.
Ya kasance abokin takarar Samia Hassan Sulubu a zaɓen shugaban ƙasa na watan Oktoban bara, wanda aka samu takaddama a kansa tare da rikicin da ya biyo bayan zaɓen.
An kashe daruruwan mutane bayan zaɓe
Samia da Nchimbi an rantsar da su a watan Nuwamba bayan samun nasarar da aka bayyana cewa sun samu kashi 98 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa.
Sai dai zanga-zangar da ta biyo bayan zaɓen ta yi sanadin mutuwar akalla mutane 500, a cewar wani bincike na hukuma, cewar rahoton tashar BBC.

Kara karanta wannan
Atiku ya ɗauki zafi, ya sake fallasa abin da yan Najeriya ba su sani ba kan tallafin man fetur
Jam’iyyun adawa da ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam sun zargi jami’an tsaro da amfani da ƙarfi wajen murƙushe masu zanga-zangar adawa da gwamnati.

Source: Instagram
Nchimbi ya ce ya cika alkawari
A cikin wasiƙar murabus ɗinsa, Nchimbi ya ce ya gamsu cewa Shugaba Samia na son yin wasu sauye-sauye, don haka ya yanke shawarar cika alkawarin da ya taɓa yi mata.
Ya ce a baya ya yi alkawarin cewa zai sauka daga mukamin idan shugaban ƙasar na son samun wani mataimaki.
Nchimbi ya gode wa Samia da jam’iyyar Chama Cha Mapinduzi (CCM) saboda amincewar da suka nuna masa, tare da godiya ga al’ummar Tanzania bisa goyon bayan da suka ba shi a lokacin da yake aikin gwamnati.
Ya ce ya yi murabus ne bisa tanadin kundin tsarin mulkin ƙasar, kuma zai ci gaba da kasancewa ɗan ƙasa nagari na Tanzania.
Ya yi kira da a samar da sabon kundin tsarin mulki
A makonnin baya, Nchimbi ya yi wasu kalamai masu tayar da hankali a siyasar ƙasar, waɗanda ake ganin ka iya zama alamun rashin jituwarsa da Shugaba Samia.
A watan da ya gabata, ya yi kira ga ‘yan Tanzania da su “yi gwagwarmayar sabon kundin tsarin mulki”, yana mai cewa akwai damar samar da sabon kundin kafin shekarar 2030.
Ya kuma danganta sabon kundin tsarin mulkin da hanyoyin magance rashin adalci, ƙarfafa haƙƙin ɗan Adam, kyakkyawan shugabanci da dimokuraɗiyya.
Tarihin Emmanuel Nchimbi
Kafin zama mataimakin shugaban ƙasa, Nchimbi ya taɓa riƙe mukamin babban sakataren jam’iyyar CCM.
Ya kuma riƙe manyan mukaman gwamnati daban-daban, ciki har da Ministan Yaɗa Labarai da Ministan Harkokin Cikin Gida.
Daga baya ya zama jakadan Tanzania a Brazil, sannan ya riƙe matsayin jakadan ƙasar a Masar kafin daga bisani ya zama mataimakin Shugaba Samia.
Hadimin gwamna ya yi murabus
A wani labarin kuma, kun ji cewa hadimi na musamman ga gwamnan Benue, Alia Hyacinth kan harkokin matasa da yaɗa labarai, Atu Terver Joseph, ya yi murabus.
Joseph ya yi murabus daga muƙaminsa ba tare da bata lokaci ba, yana mai bayyana cewa ya ɗauki matakin ne saboda dalilai na ƙashin kansa.
Asali: Legit.ng

