An hana wasu mata musulmai masu hijabi yin rajistan katin dan kasa, kungiyoyi sun koka

An hana wasu mata musulmai masu hijabi yin rajistan katin dan kasa, kungiyoyi sun koka

- Kungiyoyin musulmi sun yi korafi kan yadda ake hana mata musulmi yin rajistan katin dan kasa saboda sun saka hijabi

- Hadakar kungiyoyin sunyi wannan koken na wurin taron ranar Hijabi na duniya (1 ga watan Fabrairu) inda suka yi kira ga hukumomi a Nigeria su dauki matakin hana wannan

- Kungiyoyin sun jadadda cewa kundin tsarin mulkin Nigeria ya bawa mata musulmi damar saka hijabi kuma ba dole sai sun cire za a iya daukan hotonsu ba idan dai fuska zai fito

A kalla kungiyoyin musulmi 15 a Najeriya a ranar Litinin sun koka kan yadda ake cigaba da cin zarafin mata masu saka hijabi, inda suka ce an hana da dama cikinsu yin rajistan katin dan kasa, NIMC, da UTME da bankuna da wasu wuraren daukan bayanai, Daily Trust ta ruwaito.

Sunyi kira ga hukumomin gwamnati, kamfanoni masu zaman kansu da makarantu su dena musgunawa da cin mutuncin mata masu saka hijabi domin gwamnatin tarayya da na jihohi da kudin tsarin mulkin kasa basu haramta amfani da hijabi ba.

An hana wasu mata musulmai masu hijabi yin rajistan katin dan kasa, kungiyoyi sun koka
An hana wasu mata musulmai masu hijabi yin rajistan katin dan kasa, kungiyoyi sun koka. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: EFCC ta kama Shugaban Jami'ar Tarayya ta Gusau kan almundahar kwangilar N260m

A wani taron manema labarai na hadin gwiwa a yayin da ake bikin ranar Hijabi ta duniya a duk ranar 1 ga watan Fabrairun kowanne shekara, hadakar kungiyoyin sun ce a cikin watan Fabrairu suna shirin tattaro mutane miliyan 1 a dandalin sada zumunta domin neman kawo karshen musgunawa masu saka hijabi.

Kungiyoyi da suka hada da Kungiyar kare hakkin masu saka hijabi, Criterion, FOMWAN, NASFAT, MPAC, MURIC, Al-Mumunaat, Kungiyar mata kwararru da sauransu sun lissafa korafe-korafe da aka samu na musgunawa mata masu Hijabu a wuraren rajistar NIN da wasu wuraren.

Kungiyar ta yi kira ga gwamatin tarayya da na jihohi da majalisun kasa da bangaren shari'a da sauran hukumomin da abin ya shafa su tabbatar an dena musgunawa mata musulmi saboda kawai suna saka hijabi.

Wani sashi cikin jawabin da ta yi a madadin sauran kungiyoyin, wacce ta kafa Hijab Rights Advocacy Group, Barr. Mutiat Orolu ta ce, "Kotu ta tabbatar cewa saka hijabi ya yi dai-dai da sashi na 38(1) na kundin tsarin mulkin 1999 (da aka yi wa kwaskwarima) don haka hakki ne na yan kasa. Hana matan musulmi saka hijabi ya saba doka."

Ta kara da cewa kudin tsarin mulki da dokar hukuma NIMC ta ce,"Idan mutum ya rufe fuskarsa saboda addini (misali Hijabi) ko saboda lalural lafiya (misalin bandejin ido) ana iya amincewa da hotonsa muddin za a iya gani daga goshinsa zuwa karkashin mukamukinsa sun fito amma duk da haka ana tilastawa mata musulmi tube hijabinsu gaba daya wurin yin fasfo na fita kasashen waje.

A wani labarin daban, tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya goyi bayan Muhammadu Buhari a shekarar 2015 duk da cewa ya san 'bai san komai ba' Olagunsoye Oyinlola, tsohon gwamnan jihar Osun ya ce.

Mista Oyinlola ya yi bayanin cewa Mista Obasanjo ya yanke shawarar goyon bayan Mista Buhari ne saboda takaicin gwamnatin Goodluck Jonathan.

Duk da cewa (shi) Obasanjo ya san cewa dan takarar na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ba zai iya tabuka wani abin azo-a-gani ba, amma duk da haka ya goyi bayansa bayan wasu jiga-jigan yan Najeriya sun matsa masa lamba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164