Yan Ta'adda Suna Shirin Kai Hari Amurka, Birtaniya Ta Yi Gargadi

Yan Ta'adda Suna Shirin Kai Hari Amurka, Birtaniya Ta Yi Gargadi

  • Gwamnatin Birtaniya ta ce tana da tabbas wasu gungun yan ta'adda na shirin kai hare-hare a Amurka
  • Hakan yasa gwamnatin Birtaniya, cikin sanarwar shawarwari ga matafiya, a ranar Juma'a 4 ga watan Nuwamba ta gargadi yan kasarta da ke Amurka su yi taka tsantsan kuma su rika sauroron kafafen watsa labarai
  • Gwamnatin ta bayyana cewa wadanda za su kai harin mutane ne wadanda suka yi imani da akidar yan ta'adda

Birtaniya - Kasar Birtaniya cikin sanarwar bada shawarwari ga masu tafiye-tafiye ga yan kasarta, a ranar Juma'a ta yi gargadin cewa yan ta'adda na shirin kai hari Amurka.

Ta shawarci yan kasarta da ke Amurka su yi taka tsantsan kuma su guji zuwa wuraren taruwan mutane, The Nation ta rahoto.

Sunak
Birtaniya Ta Gargadi Amurka Cewa Yan Ta'adda Na Shirin Kawo Mata Hari. The Nation.
Asali: Facebook

Wuraren da ake zargin yan ta'addan za su kai harin a Amurka, in ji Birtaniya

Kara karanta wannan

Tsaiko ga daliban Najeriya yayin da ASUU ke shirin komawa yajin aiki saboda dalili 1

A cewar Birtaniya, akwai yiwuwar yan ta'addan za su kai hari inda baki ke taruwa ko wuraren taruwar mutane da tashohin zirga-zirga.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A baya-bayan nan, Legit.ng ta rahoto cewa Amurka da Birtaniya sun gargadi yan kasarsu cewa akwai yiwuwar yan ta'adda za su kawo hari Abuja.

Vanguard ta rahoto cewa hukumar yan sandan FBI ta gargadi Amurkawa a New Jersey cewa yan ta'addan na shirin kai hari a wuraren ibadu.

FBI ta ce ta samu sahihin bayanin sirri game da barazanar kai hari a wuraren bauta a New Jersey tana mai kira su dauki matakin kare iyalansu.

Sanarwar ta ce:

"Akwai yiwuwar yan ta'adda za su kawo hari a Amurka. Ana iya kai harin a ko, ciki har da wuraren da baki ke zuwa, wurin taruwa mutane da cibiyoyin sufuri. Ku rika duba kafafen watsa labarai kuma ku zama masu taka tsantsan.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Bude Wa Mutane Wuta Ana Tsaka da Cin Kasuwa, Sun Tafka Barna a Jihar Arewa

"Babban barazanar ta fito ne daga daidaikun mutane wadanda watakila akidar ta’addanci ta sanya su kai hare-hare da ake kira ‘Harin kai kadai’ da ake kaiwa kan al’umma ko wurare. Hare-hare na iya faruwa ba tare da an lura ba."

Dangane da gargadin, gwamnatin Birtaniya ta ce akwai yiwuwar Amurka za ta tura jami'an tsaro zuwa wuraren taruwar mutane don dakile yiwuwar kai harin, ta kara da cewa hukumar tsaro ta Homeland ta fitar da gargadi mai inganci game da yiwuwar harin.

Ba Sojojin Amurka Ne Suka Kai Samame A Abuja Ba, In Ji Mazaunin Unguwa

A wani rahoton, kun ji cewa sojojin Amurka ba su cikin wadanda suka kai samame a rukunin gidaje na Trademore da ke Lugbe, babban birnin tarayya, Abuja, in ji wani mazaunin unguwar, Daily Trust ta rahoto.

Mazaunin, wanda ya tabbatar an kawo samame unguwar, ya ce kawai dan kasar waje daya aka gani cikin jami'an da suka kawo samamen.

Kara karanta wannan

Bayan Abuja, Jami'an EFCC Sun Kai Simame Shagunan Yan Canji a Jihar Kano

Asali: Legit.ng

Online view pixel