Paul Biya Ya Lashe Zaben Shugaban Kasar Kamaru na 2025
- Hukumomi a kasar Kamaru mai makwabtaka da Najeriya sun sanar da sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar
- Sakamakon zaben ya fito ne a ranar Litinin, 27 ga watan Oktoban 2025 kwanaki bayan an gudanr da shi a fadin kasar
- Shugaban kasa Paul Biya ya doke babban abokin hamayyarsa, Issa Bakary Tchiroma, wanda ya zo na biyu a fafatawar da aka yi
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Kasar Kamaru - Hukumomi a kasar Kamaru sun sanar da sakamakon zaben shugaban kasa wanda Shugaba Paul Biya, ya kasance daga cikin 'yan takara.
An bayyana Shugaba Paul Biya, mai shekaru 92, a hukumance a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa na 2025, wanda aka gudanar ranar 12 ga Oktoba.

Source: Twitter
Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa majalisar kundin tsarin mulkin kasar ce ta sanar da sakamakon zaben a hukumance ranar Litinin, 27 ga watan Oktoban 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Paul Biya ya sake lashe zaben Kamaru
A sakamakon zaben da aka fitar, Shugaba Paul Biya ya samu 53.66% na luri’un da aka kada, yayin da babban abokin hamayyarsa, Issa Tchiroma, ya samu k35.19%.
Da wannan nasara, Paul Biya, wanda ya shafe shekaru da dama yana mulkin Kamaru tun daga 1982, zai ci gaba da jagorancin kasar na tsawon shekaru bakwai masu zuwa.
Paul Biya, wanda yanzu yake da shekaru 92, ya ci gaba da zama shugaban kasa mafi tsufa da ke kan mulki a duniya, kuma zai ci gaba da mulki har zuwa shekara ta 2032, rahoton BBC News ya tabbatar da hakan.

Kara karanta wannan
Zargin kisan Kiristoci: Babachir ya fasa kwai kan rawar da Buhari da Tinubu suka taka
Dan adawa ya zo na 2 a zaben Kamaru
Ko da yake ɗan takarar adawa Issa Tchiroma Bakary ya samu gagarumin goyon baya daga ‘yan Kamaru da ke kasashen waje, kuri’un cikin gida sun bai wa Paul Biya nasara mai karfi.
A kasashen Turai, Tchiroma ya samu kashi 62.79% na kuri’un da aka kada, yayin da Paul Biya ya samu kashi 22.63% kawai.
A kasashen yankin Americas, Tchiroma ya samu kashi 66.75%, sannan a Asiya da Gabas ta Tsakiya, ya samu kashi 68.21%.
Haka kuma a nahiyar Afirka, Tchiroma na kan gaba a kuri’un mazauna kasashen waje da kaso 54.99%, duk da cewa fiye da rabin masu cancantar kada kuri’a ba su fito ba.
Sai dai, majalisar kundin tsarin mulki ta bayyana cewa wanda zai ci zabe ana kayyade shi ne bisa jimillar kuri’un da aka kada gaba ɗaya, ba bisa ga yankuna ko kuri’un mazauna kasashen waje kaɗai ba.

Source: Getty Images
Nasarar Paul Biya ta zo ne a lokacin da ake kara samun kiraye-kirayen neman sauyin siyasa a Kamaru, inda masu sukar gwamnati ke zargin jam’iyyar mai mulki da danne adawa da kuma tafka magudi a zabe.
Sai dai gwamnatin Kamaru ta jaddada cewa zaben ya gudana cikin ‘yanci da gaskiya.
Da wannan nasarar, Paul Biya zai ci gaba da jagorantar kasar har sai ya kai shekaru 99 a duniya, sai dai idan an samu sauyin tsarin mulki ko wani lamari da ba a yi tsammani ba.
Tchiroma ya yi ikirarin lashe zaben Kamaru
A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar jam'iyyar adawa a zaben shugaban kasar Kamaru, Issa Tchiroma Bakary, ya yi ikirarin lashe zabe.
Issa Tchiroma Bakary ya bayyana cewa zai fitar da rahoton asali na yadda sakamakon yake a rumfunan zabe.
'Dan takarar shugaban kasan ya ce matakin nasa na nufin tabbatar da gaskiya da kaucewa duk wani yunkuri na karkatar da sakamakon zaben.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

