Kungiyar Lauyoyi Musulmai sun mara goyon bayansu kan hukuncin kisa ga mai batanci ga Manzon Allah

Kungiyar Lauyoyi Musulmai sun mara goyon bayansu kan hukuncin kisa ga mai batanci ga Manzon Allah

Kungiyar Lauyoyi Musulmai a jihar Kano (MULAN), ta yabwa kotun Shari'ar Musulunci kan yankewa Yahaya Sharif Aminu hukuncin kisa kan kalaman batanci ga manzon Allah (SAW)

Kungiyar Lauyoyin a takardar da shugabanta, Muhammadu Sani Garba, ya saki, ya ce Alkalin ya yi daidai a hukuncin da ya yanke na kisa ba tare da hanashi iya daukaka kara ba saboda kotun koli ta yanke irin hukuncin a shari'ar Abubakar Shalla Vs State a 2007.

Kungiyar MULAN ta yi kira ga gwamna Ganduje ya rattafa hannu kan hukuncin, amma har yanzu gwamnan bai yi tsokaci ba.

Shugaban MULAN yace: "Abinda dokar Shari'ar Musulunci ta tanada shine duk wani Musulmi baligi, wanda ya zagi manzon Allah, ko kalaman batanci ga manzon Allah, ya aikata laifi mai girma kuma ya cancanci kisa."

"Gama-garin jama'a su fahimci cewa Shari'ar Musulunci na aiki ne kan Musulmai kadai. Duk wanda ya amince ya zama Musulmi wajibi ne yayi biyayya ga Shari'ar, ko ta yi masa dadi, ko batayi ba."

"Wadanda ba Musulmai ba su fahimci cewa kundin tsarin mulkin Najeriya ta amincewa yan Najeriya su yi addinin da suka zaba kuma su bi dokokin addini."

"Muna kira ga gwamnatin jihar Kano ta tabbatar da cewa an zartar da hukuncin, saboda nuna tana da niyyar aiwatar da Sharia"

Kungiyar Lauyoyi Musulmai sun mara goyon bayansu kan hukuncin kisa ga mai batanci ga Manzon Allah
Kungiyar Lauyoyi Musulmai sun mara goyon bayansu kan hukuncin kisa ga mai batanci ga Manzon Allah
Asali: UGC

A ranar Litinin da ta gabata ne wata kotun shari'ar Musulunci ta yankewa wani matashi mai suna Sharif-Aminu hukuncin kisa ta hanyar rataya sakamakon batanci da ya yi ga Annabi Muhammadu.

Duk da matashin yana da kwanaki 30 don daukaka karar matukar bai gamsu da hukuncin ba, shugaban majalisar malamai, Sheikh Muhammad Nasir Adam, ya ce gwamnati ta gaggauta saka hannu a kan hukuncin kotun ba tare da duban siyasa ba.

Adam, wanda ya zanta da manema labarai a Kano, ya jinjinawa kotun da ta yanke wannan hukuncin kuma ya ce hakan ne Musulunci ya tanadar.

A martanin shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN), Adeolu Samuel Adeyemo, ya ce batanci a addinin Kirista laifi ne da ba a taba yafe shi kuma babu kirista nagari da ya dace ya aikata don karantsaye ne ga dokokin Ubangiji.

Duk da shugaban CAN ya ce wannan hukuncin na Shari'a ne ta Musulunci, ya ce dole ne a jaddada shi idan ana neman zaman lafiya a tsakanin al'umma.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel