Amurka Ta Yi Gargadi da Ta Hango Hadari Mai Girma a Kasashen Afirka 11, Ta Jero Sunayensu

Amurka Ta Yi Gargadi da Ta Hango Hadari Mai Girma a Kasashen Afirka 11, Ta Jero Sunayensu

  • Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta sanya ƙasashen Afirka 11 cikin jerin wuraren da ta gargadi ‘yan ƙasarta kada su je
  • Ƙasashen sun haɗa da Burkina Faso, Nijar, Mali, Libya, Sudan da Uganda, sakamakon matsalolin ta’addanci
  • Najeriya ba ta cikin jerin ƙasashen 11, amma Amurka na ci gaba da ba da shawarar a sake tunanin tafiya zuwa ƙasar saboda matsalolin tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Amurka - Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta sanya ƙasashen Afirka 11 cikin matsayi mafi girma na gargadin tafiye-tafiye ga Amurkawa.

Sakamakon haka, ta shawarci ‘yan ƙasar Amurka da kada su ziyarci wadannan kasashe saboda barazanar tsaro da ƙarancin damar ba da agajin gaggawa.

Shugaba Trump.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump a fadar White House Hoto: Anadolu
Source: Getty Images

Vanguard ta ruwaito cewa wannan gargadi na cikin wani babban jerin da ya ƙunshi ƙasashe 23 a sassan duniya, wanda ofishin kula da harkokin jakadanci na ma’aikatar ya sanar a ranar Litinin, 9 ga Nuwamba, 2026.

Kara karanta wannan

Atiku ya ce ya gano tarkon da Tinubu ya kafa masa kan bashin da zai ci a waje

Jerin sunayen kasashen Afirka 11

Ƙasashen da abin ya shafa a Afirka su ne:

1. Burkina Faso

2. Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

3. Chadi

4. Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DRC)

5. Libya

6. Mali

7. Nijar

8. Somaliya

9. Sudan ta Kudu

10. Sudan

11. Uganda.

A cikin bayanin da ma’aikatar ta fitar, ta ce:

“Mataki na 4 na nufin kada a je. Muna sanya ƙasa a wannan matsayi bisa la’akari da yanayin wurin da kuma ƙarancin damar da muke da ita na taimaka wa Amurkawa a can. Waɗannan wurare na da haɗari. Kada ku je ko da wani dalili.”

Ƙasashen Afirka da ke cikin jerin na fuskantar matsalolin tsaro daban-daban, ciki har da ta’addanci, rikicin kwararar makamai, garkuwa da mutane, rashin kwanciyar hankali a siyasa, aikata laifuka da tarzoma.

Abin da ke faruwa a wasu kasashen

Burkina Faso da Mali na ci gaba da fuskantar barazanar ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai da tsattsauran ra’ayi, musamman a wasu sassan yankin Sahel.

Kara karanta wannan

Barayi sun shiga masallaci sun sace fankoki sama da 20 a Kano

Jamhuriyar Nijar da Chadi ma na fuskantar barazanar ƙungiyoyin mayaka da ke aiki a yankin, tare da matsalolin siyasa da tsaro.

Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ta shafe tsawon lokaci tana fama da rashin tsaro sakamakon ayyukan ƙungiyoyin yan ta'adda, yayin da Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo kuwa, rikici na ci gaba da addabar gabashin ƙasar.

Somaliya na ci gaba da fuskantar hare-haren mayaka, musamman waɗanda ke da alaƙa da ƙungiyar Al-Shabaab. Haka kuma, ana samun barazanar garkuwa da mutane da sauran matsalolin tsaro.

Sudan na cikin manyan ƙasashen Afirka da rikici ya fi shafa tun bayan barkewar yaƙi tsakanin rundunar sojin ƙasar da ƙungiyar rundunar kai ɗaukin gaggawa (RSF) a watan Afirilu na 2023.

Jirgi.
Jirgin sama yana kan hanya a sararin samaniya Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Sai dai gargadin ba ya nufin cewa an hana ‘yan ƙasashen da aka lissafa shiga Amurka. Gargadin ya shafi ‘yan ƙasar Amurka ne.

Najeriya ba ta cikin ƙasashen Afirka 11 da aka sanya a mataki na 4. Sai dai har yanzu Amurka na sanya ƙasar a mataki na 3, wato shawarar sake tunanin tafiya zuwa Najeriya.

Najeriya ta ja hankalin yan kasar a Faransa

Kara karanta wannan

Magana ta kare: Trump ya yi maganar yiwuwar sake kai hare hare a Iran

Kun ji cewa hukumar NiDCOM ta bukaci ’yan Najeriya da ke zaune a Faransa su kwantar da hankula tare da guje wa tashin hankali yayin da ake gudanar da zanga-zanga a ƙasar.

Hukumar ta kuma bukaci ’yan Najeriya su mutunta maƙwabtansu da sauran al’ummomi ba tare da la’akari da ƙasa, addini ko asalin mutum ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262