Amnesty Ta Bukaci a Kama 'Yan Daban da Suka kai wa Pantami Hari a Gombe

Amnesty Ta Bukaci a Kama 'Yan Daban da Suka kai wa Pantami Hari a Gombe

  • Amnesty International ta yi Allah wadai da harin da wasu ’yan daba suka kai wa tawagar yakin neman zaben PDP a Gombe ranar 11 ga Nuwamba, 2026
  • Kungiyar ta ce tana zargin maharan da hannu a jam’iyyar APC, inda ta bukaci jami’an tsaro su gudanar da bincike tare da hukunta wadanda aka samu da laifi
  • A daya bangaren kuma. rundunar ’yan sandan Gombe ta tabbatar da faruwar lamarin, amma ta ce ba ta kama wani mutum ba kawo yanzu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Gombe – Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta yi Allah wadai da harin da wasu ’yan daba da ake zargi da siyasa suka kai wa tawagar yakin neman zaben dan takarar gwamnan jihar Gombe na jam’iyyar PDP, Sheikh Isa Ali Pantami.

Kara karanta wannan

Kwana 2 kafin ziyarar Tinubu, 'yan bindiga sun kewaye gari sun buɗe wa mutane wuta

Harin ya faru ne a ranar Laraba, 11 ga Nuwamba, 2026, a kan titin Jekadafari da ke cikin garin Gombe, a lokacin da tawagar Pantami ke kokarin shiga birnin.

Sheikh Isa Ali Pantami
Sheikh Pantami a wajen taron PDP. Hoto: Abba Sani Pantami
Source: Facebook

A cikin sanarwar da ta fitar a Facebook, Amnesty International ta ce harin ya yi kama da yunkurin hana dan takarar shiga garin Gombe ta hanyar amfani da tashin hankali.

An zargi 'yan APC da kai hari

Kungiyar ta ce binciken da ta gudanar ya nuna zargin cewa maharan na aiki ne da goyon bayan wasu da ke da alaka da jam’iyyar APC.

Bidiyoyin da suka bazu a kafafen sada zumunta sun nuna wasu gungun mutane dauke da makamai, suna tare hanya da tayoyi kafin su cinna musu wuta.

Haka kuma, an ga yadda aka farfasa gilasan motocin da ke cikin tawagar, lamarin da ya kawo tsaiko ga zirga-zirgar abubuwan hawa a yankin.

Amnesty International ta bayyana lamarin a matsayin daya daga cikin munanan hare-haren siyasa da aka gani tun bayan fara shirye-shiryen yakin neman zaben 2027.

Kungiyar ta bukaci a yi bincike

Amnesty International ta bukaci jami’an tsaro su gudanar da cikakken bincike domin gano wadanda ke da hannu a harin tare da gurfanar da su a gaban kotu bisa tsarin shari’a na gaskiya.

Kara karanta wannan

Pantami ya shiga Gombe duk da kona tayoyi, toshe hanya da kai masa hari

Ta kuma nuna damuwa kan rashin kama wani mutum da ake zargi da hannu a tashin hankalin, tana mai cewa babu wata hujja da ta nuna an kama wadanda suka aikata laifin kawo yanzu.

Kungiyar ta yi gargadin cewa ci gaba da kai wa ’yan adawa hare-hare zai iya hana su gudanar da harkokin siyasa cikin lumana.

Ta jaddada cewa tashin hankali ba shi da gurbi a tsarin dimokuradiyya, inda ta bukaci dukkan jam’iyyun siyasa su gargadi magoya bayansu kan guje wa duk wani nau’in rikici.

Sheikh Isa Ali Pantami
Lokacin da Sheikh Isa Ali Pantami ya isa jihar Gombe. Hoto: Abba Sani Pantami
Source: Facebook

’Yan sanda sun tabbatar da harin

A nata bangaren, Punch ta wallafa cewa rundunar ’yan sandan jihar Gombe ta tabbatar da harin da aka kai wa tawagar Pantami a yankin Jekadafari.

Kakakin rundunar, Buhari Abdullahi, ya bayyana cewa harin ya faru ne lokacin da Pantami ya isa jihar, inda daruruwan magoya bayansa suka tarbe shi a fadar mai martaba Sarkin Gombe.

A cewarsa, an samu kone-konen tayoyi da kuma lalata gilasan motocin a yayin da jama’a suka taru domin tarbar dan takarar da kuma gabatar wa ’yan takarar tutocin jam’iyyunsu.

PDP ta kafa kwamitin kamfen

Kara karanta wannan

2027: Alƙawurran da Sheikh Pantami ya ɗauka a tsakiyar dandazon mutane a Gombe

A wani labarin, mun ruwaito cewa jam’iyyar PDP reshen jihar Gombe ta sanar da kafa kwamitin yakin neman zabenta na babban zaben shekarar 2027.

Jam’iyyar ta bayyana cewa Sanata Haruna Garba, wanda aka fi sani da Magayakin Gombe, ne zai jagoranci kwamitin, yayin da Sanata Ibrahim Hassan Dankwambo, zai kasance mataimakin shugaban kwamitin.

PDP ta ce za a fitar da sunayen mambobi 2,000 da aka nada domin aiki a daraktoci, kwamitoci da kuma kananan hukumomi, inda za su taimaka wajen tsara tare da gudanar da ayyukan kamfen.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng