Da taimakon Rasha, kasar Syria ta kakkano daruruwan manyan makamai masu linzami da Turai da Amurka suka harba mata

Da taimakon Rasha, kasar Syria ta kakkano daruruwan manyan makamai masu linzami da Turai da Amurka suka harba mata

- An harba akalla mizayil (Missile) 100 kan kasar Siriya

- Amurka da kawayenta na kokarin ganin sun kakkabe kokarin Assad na amfani da makamai da aka harammta kan mutanensa

- An kai harin gubar ne a makon jiya, amma Rasha ta kare Assad din ta karyata harin

Da taimakon Rasha, kasar Syria ta kakkano daruruwan manyan makamai masu linzami da Turai da Amurka suka harba mata

Da taimakon Rasha, kasar Syria ta kakkano daruruwan manyan makamai masu linzami da Turai da Amurka suka harba mata

Bayan da gwamnatin Basshar Al-Asad ta kai hare-hare da makamai kan jama'ar Siriya dake son lallai sai yabar mulki, masu guba wanda duniya tayi wa Allah-Wadai, da wannan mummunan hari da son mulki wanda ya gada daga babansa Hafez.

Shi dai Basshar Al-Asad, ya hau mulkin ne a 2000 bayan da mahaifinsa ya rasu, kuma yaki barin mulkin inda yake son shima sai ya rayu din-dindin a matsayin shugaba.

Sai dai kasar mai yawan kabilu, Sunni, Shia da Kurdawa, ta fada yakin basasa tun a guguwar 2011, kum a abin yaki ci yaki cinyewa.

DUBA WANNAN: Ko Buhari ya yarda yanzu Abacha ya kwashe kudin Najeriya a mulkinsa?

Kasashen Iran da Rasha suna mara wa mulkin nasa baya, sauran kuma larabawa sunni suna mara wa masu tawaye baya,, wadanda yawancin su Sunni ne, kuma an sami masu tsattsauran ra'ayi cikinsu.

Bayan harba akalla manyan missile 100, masu linzami kan karfin sa na soji, sansanonin hada makamai masu guba, da ma barikokin ajje makamai, da taimakon Rasha, asar ta harbo akalla 70 cikin dari na makaman da aka harbo, da irin nasu missile din kirar Rasha, SAM, watau Surface to Air- Missile.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel