Girgizar Kasar Turkiyya-Syria: Sama da Mutum 44,000 Sun Rasa Rayukansu

Girgizar Kasar Turkiyya-Syria: Sama da Mutum 44,000 Sun Rasa Rayukansu

  • Gagarumar girgizar kasa ta ritsa da jama'a a kasashen Turkiyya da Syria inda aka tabbatar da mutuwar sama da mutane 44,000
  • Har yanzu ana cigaba da aikin ceto wanda yuwuwar ciro jama'a da ransu yana raguwa
  • Shugaban kasar Turkiyya, Erdogan, ya sanar da cewa 'yan matsaloli aka samu amma yanzu an shawo kansu ana cigaba da ceton

Sama da mutane 44,000 ne aka tabbatar da mutuwarsu bayan gagarumar girgizar kasa da ta fadawa Turkiyya da Syria a kawo ranar Asabar, rahoton ChannelsTV.

Girgizar kasa
Girgizar Kasar Turkiyya-Syria: Sama da Mutum 16,000 Sun Rasa Rayukansu. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

A makon baya Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta ja kunnen cewa ta yuwu yawan mace-macen ya kai 20,000 yayin da ake ceto jama;a da dubban gine-gine suka murkushe ana tsaka da sanyi.

Girgizar kasar da aka jia kasashe masu makwabtaka yana daya daga cikin mafi karfin girgizar kasa da aka yi a yankin sama da shekaru 100 da suka shude.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Matashi Dan Shekara 20 Ya Yi Garkuwa Da Mahaifiyarsa A Zamfara, Ya Karbi Miliyan 30 Kudin Fansa

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kwararru sun ce tsawon lokaci da wadanda suke kasan kasar za su iya dauka a fito dasu a raye ko babu rai yana matsowa.

Sama da kashi 90 na wadanda ake cetowa daga girgizar kasa kuma su rayu ana ceto su ne cikin kwanaki ukun farko.

"Sa'o'i 72 na farko suna da matukar amfani."
"Yawan wadanda ke fitowa da ransu cikin sa'o'i 24 shi ne kashi 74, bayan sa'o'i 72 kashi 22 ne da kuma kashi shida a rana ta biyar."

- CBS News ta tsakuro daga abinda Steven Godby, kwararre daga jami'ar Nottingham Trent a Ingila yace.

Ana ta cece-kuce kan yadda gwamnatin kasar Turkiyya ke martani a hankali kan wannan ibtila'in.

Shugaban kasa Recep Erdogan na kasa Turkiyya yace an samu wasu matsaloli ne da farko a filin jirgin sama da tituna amma ya jaddada cewa yanzu an shawo kan lamarin.

Kara karanta wannan

Karancin Kudi: Gwamna Ya Samar Da Bas Din Kyauta Don Ragewa Al'ummarsa Radadin Halin Da Ake Ciki

Matar auri ta haifa jinjiri da IUD a hannu

A wani labari na daban, matar aure ta haifa jinjiri rike da IUD din da tayi amfani da shi don gujewa daukar ciki.

Tace ita da mijinta sun yi aure amma basu shirya haihuwa ba, hakan yasa ta nemi mafita amma sai da ta haihu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel