An Kashe Tsohon Shugaban Iran, Ahmadinejad a Yaƙin da Ake Yi? An Samu Bayanai

An Kashe Tsohon Shugaban Iran, Ahmadinejad a Yaƙin da Ake Yi? An Samu Bayanai

  • An yi ta yada jita-jita ta yadu cewa an kashe tsohon shugaban Iran, Mahmoud Ahmadinejad a Tehran, lamarin da ya jefa jama'a cikin rudani
  • Rahotanni sun ce harin "na kwararru" ne, yayin da kafofin sada zumunta suka riƙa yada labarin mutuwarsa tare da iyalinsa
  • Daga baya gwamnati ta karyata jita-jitar, ta tabbatar da cewa "Ahmadinejad yana raye, kuma babu wani yunkurin kashe shi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Tehran, Iran - Gwamnatin kasar Iran ta yi martani kan rade-radin kisan tsohon shugabanta da ake ta yaɗawa musamman a kafofin sadarwa.

An saka mutane a cikin rudani kan labarin cewa an kashe Mahmoud Ahmadinejad yayin da ake ci gaba da yaki tsakanin Iran da Isra'ila.

Gwamanti ta yi martani kan rade-radin kashe Ahmadinejad
Gwamnatin Iran ta musanta labarin kashe Mahmud Ahmadinejad. Hoto: @ub18r/X.
Asali: Twitter

Rahoton Gulf Today ya ce labarin ya nuna cewa an hallaka Ahmadinejad ne a birnin Tehran ta hannun wasu da ba a san ko su waye ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda zargin labarin mutuwar Ahmadinejad ya watsu

Sai dai a rahoton, an bayyana cewa ana zargin harin na kwararru ne wanda ya tayar da hankulan al'umma.

Kafofin sada zumunta sun rude da rubuce-rubucen da suka karade dandalin da cewa: “An kashe Ahmadinejad da iyalinsa."

Wasu ko cewa suke yi “Mossad ta sake kai hari,” “An killace birnin Tehran” da sauransu.

Jita-jitar ta zo daidai da karuwar tashin hankali tsakanin Iran da Isra’ila, ciki har da barazanar kai hari daga Tel Aviv har cikin kasar Iran.

An ƙaryata labarin cewa an hallaka Ahmadinejad
Gwamnatin Iran ta musanta labarin cewa an kashe Mahmoud Ahmadinejad. Hoto: @Getty Images.
Asali: Twitter

Menene gaskiyar abin da ya faru da Ahmadinejad?

Amma ana cikin wannan rudani, gwamnati ta fitar da sanarwa cewa Ahmadinejad yana raye, kuma babu wani yunkurin kashe shi da aka yi.

Wannan labari mara tushe ya haifar da ruɗani mai yawa da kuma alamar tambayoyi kan dalilan kawo shi a daidai wannan lokaci.

Wasu na tambayar ko wani yunkuri ne na dabarun yaƙi wurin aiki da basira da nufin bude kofa ga sauye-sauyen siyasa na yankin?

A halin yanzu dai, abu daya ne kadai aka tabbatar da shi, tsohon shugaban kasar, Mahmoud Ahmadinejad bai mutu ba, cewar rahoton Roya News.

Alburusai na farko ba daga bindiga suka fito ba, sai dai daga fagen fama na yaɗa ƙarya, wanda ya bar tambayoyi marasa amsa.

Hakan shi ke tabbatar da cewa tsohon shugaban yana nan raye sabanin rahotanni da ake yaɗawa a cikin yan kwanakin nan.

Dubban Yahudawa na tserewa daga Isra'ila

Mun ba ku labarin cewa dubban Yahudawan Isra'ila aƙalla 8,000 sun rasa gidajensu da ƙasar Iran ta ci gaba da kai hare-haren ramuwar gayya tun makon jiya.

Rahotanni daga Isra'ila sun tabbatar da cewa mutane sama da 30,000 suka shigar da buƙatun neman diyyar gine-ginesu da aka rusa yayin yakin da ake yi.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa a yau Juma'a, 20 ga watan Yuni, 2025 aka shiga rana ta takwas tun bayan fara musayar wuta tsakanin Iran da Isra'ila.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.